'An Ci Fuskar Doka': Hakeem Baba Ahmed Ya Soki Gwamnati kan Tsare El Rufa'i

'An Ci Fuskar Doka': Hakeem Baba Ahmed Ya Soki Gwamnati kan Tsare El Rufa'i

  • Tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya dura a kan gwamnatin tarayya byan an tsawaita tsare Nasir El-Rufa'i
  • Ya bayyana cewa an take doka wajen mayar da tsohon gwamnn jihar Kaduna 'fursunan siyasa' tare da cewa babu dokar da ta amince da ci gaba da tsare shi
  • Hakeem Baba-Ahmed yana wannan batu ne bayan sakon da iyalan El-Rufa'i suka aika ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan hidimar da aka yi masa a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya soki ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai cewa yanzu ya zama fursunan siyasa.

Kara karanta wannan

An kashe bakin tsanya, Kudan da aka 'nadi muryarsa' ya gana da El Rufa'i da ke hannun ICPC

Tsohon hadimin shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da tsare El-Rufai ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ko aka yanke masa hukunci ba.

Hakeem Baba-Ahmed ya soki gwamnati kan tsare El-Rufa'i
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana wannan damuwa ne ta cikins sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, 2026.

Hakeem Baba ya soki gwamnati saboda El-Rufa'i

A cewarsa, ci gaba da rike mutum a tsare ba tare da bin ka'idojin shari'a ba na rage wa tsarin doka kima, tare da haifar da rashin amincewa da yadda ake gudanar da adalci.

Hakeem Baba Ahmed ya ce an mayar da El-Rufa'i fursunan siyasa
Shugaba Bola Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed Hoto: Bayo Onanuga/Hakeem Baba-Ahmed
Source: Facebook

Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya yi nuni da cewa irin wannan mataki ba ya dace da tsarin dimokuradiyya da ke bai wa kowa damar samun adalci a karkashin doka.

Kalaman Baba-Ahmed sun zo ne bayan iyalan Nasir El-Rufai sun gudanar da taron manema labarai, inda suka roki gwamnatin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta sake duba lamarin.

Jama'a sun yi martani kan tsare El-Rufa'i

Kalaman Hakeem Baba-Ahmed ya ja hankulan masu bibiyarsa, inda wasu ke ganin tasirin tsohon gwamnnan a siyasar kasar nan ne ya jawo aka ci gaba da tsare shi.

Kara karanta wannan

Yadda haduwa da Peter Obi zai jawo wa Kwankwaso asarar kuri'a a 2027

@InyasiY1275 ya ce:

"El-Rufai ba mutumin kirki ba ne kamar yadda yake tunanin kansa. Ya aikata munanan abubuwa lokacin da yake kan mulki. sakayya gaskiya ce, siyasa ce ko ba siyasa ba, ya cancanci ya dade a gidan yari.

@KuteyiOlaolu ya ce:

"El-Rufai ne yake hana shari'arsa tafiya yadda ya kamata, sannan kuma yana yin irin kazamar siyasar da Kanu yake yi.

@official_alamin ya ce:

"Babu shakka tasirinsa zai sake fasalin yanayin siyasa. Shi ya sa mutane da dama ke ganin ana ci gaba da nisanta shi daga fagen siyasa domin a takaita irin tasirin da zai iya yi."

Iyalan El-Rufa'i sun tura sako ga Tinubu

A baya, mun kawo labarin cewa matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta roƙi Shugaba Tinubu game da halin da mijinta ke ciki wanda har yanzu ya ke a tsare a hannun jami'an hukumar ICPC.

Asia ta ce sun yi wa Tinubu kamfen sosai a zaɓen 2023, tana jaddada cewa ba sa neman tsoma baki, sai dai a ba El-Rufai beli mai sauƙi wanda zai ba shi damar dawo wa cikin iyalansa yayin da ake shari'a.

Iyalan tsohon gwamna El-Rufai sun zargi ana hana shi ganin likitocinsa, lauyoyinsa da 'yan uwansa, yayin da hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta kasa, ICPC ke zargin ya karya sharuɗɗan da aka sa masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng