Gbajabiamila Ya Rubuta Wasika ga PSC don Yi Wa 'Yan Sandan da Ke Tare da 'Yan Siyasa Karin Girma

Gbajabiamila Ya Rubuta Wasika ga PSC don Yi Wa 'Yan Sandan da Ke Tare da 'Yan Siyasa Karin Girma

  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya aika da wasika ga hukumar kula da ayyukan 'yan sanda (PSC)
  • Femi Gbajabiamila ya aika da wasikar ne domin neman hukumar ta yi wa wasu 'yan sanda guda takwas karin girma na musamman
  • Ana zargin cewa wannan bukata dai da Femi Gbajabiamila ya nemi ta sabawa dokar kafa hukumar PSC ta shekarar 2001

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya mika wata bukata gaban hukumar kula da ayyukan 'yan sanda (PSC).

Femi Gbajabiamila, ya buƙaci hukumar PSC da ta amince da ƙarin girma na musamman ga jami’ai takwas da ke aiki da ’yan siyasa.

Gbajabiamila ya mika bukata ga hukumar PSC
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila Hoto: Speaker Femi Gbajabiamila
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta kawo rahoto a ranar Asabar, 23 ga watan Mayun 2026 cewa Gbajabiamila ya mika bukatar ne cikin wasu wasiku.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi hasashe da ya ga yawan mutanen da suka fito zaben Tinubu

Femi Gbajabiamila ya nemi bukata wajen PSC

Bukatar, wadda ke ƙunshe cikin wasiƙu guda biyu daban-daban, ta taɗa damuwa ta fuskar doka da ɗa'a saboda dokar PSC ta mika ikon ƙarin girma ne kawai ga hukumar kanta.

A cikin ɗaya daga cikin wasiƙun da jaridar ta gani, Gbajabiamila ya buƙaci da a ba wa jami'an da ke aiki da shugaban kasar tarayyar Najeriya karin girma na musamman.

Ɗaya daga cikin wasiƙun, mai kwanan watan 20 ga watan Fabrairu, 2026, tana ɗauke da sunayen jami’ai uku, yayin da ɗayar kuma ke ɗauke da sunayen jami’ai biyar.

Bukatar ita ce a ɗaukaka jami'i ɗaya daga muƙamin ACP zuwa DCP, sannan wasu guda biyu daga CSP zuwa mukamon ACP.

Wasikar Gbajabiamila ta saba doka

Wannan mataki na shugaban ma'aikatan shugaban ƙasar ya saɓa wa tanade-tanaden dokar kafa hukumar kula da ayyukan ’yan sanda ta shekarar 2001.

A cewar sashe na shida na dokar, ikon ƙarin girma a duk faɗin rundunar yana hannun hukumar ne, ba ga wani mutum guda ba a wajen hukumar.

Kara karanta wannan

Gabbard: Babbar jami'a a gwamnatin Trump ta yi murabus

Gbajabiamila ya rubuta wasika ga PSC
Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Hoto: Speaker Femi Gbajabiamila
Source: Facebook

Jami'in 'yan sanda ya yi korafi

Wani jami’an ɗan sanda da ke da masaniya kan lamarin ya bayyana cewa shirin ƙarin girma na musamman na iya samun mummunan tasiri ga waɗanda ke yaƙi da rashin tsaro.

Ya bayyana cewa:

“A jihar Yobe, an kashe jami’an ’yan sanda 17; babu wani daga fadar shugaban ƙasa da ya kira iyalansu ko ya je yi musu ta'aziyya." “Hasali ma, sauran jami’an ’yan sandan da ke cikin waccan rundunar sun ci gaba da yaƙar Boko Haram a washegari."
"Waɗancan ba su samun ƙarin girma na musamman; ba su ma samun gaisuwa ta musamman daga shugaban ƙasa, amma waɗanda ke sarawa shugaban ƙasa, suke tuƙi a motoci masu AC, kuma suke cin abincin shugaban ƙasa, su ne ke samun ƙarin girma na shugaban ƙasa don jin daɗi."
“Idan Tinubu ya ci gaba da haka, karsashi zai ragu, kuma mutanen da ke fagen fama ba za su ga ba amfanin yakin da suke yi."

Kara karanta wannan

"Kada a zalunci El Rufa'i": Tsohon jigon APC ya roki dattawan Arewa su saka baki

Shugaba Tinubu ya titsiye Gbajabiamila

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana yadda ta kaya tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kira shi zuwa gidansa da ke Abuja domin tambayarsa ko Desmond Elliott na daga cikin mutanen da ke haddasa rikicin tsige shugaban majalisar dokokin jihar Legas.

Gbajabiamila ya ce ya tabbatar wa shugaban kasa cewa Desmond Elliott yaronsa ne kuma bai yi imanin yana cikin masu tayar da rikicin ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng