Ma'aikatar Bogi: Kujerun Manyan Jami'an Tinubu na Rawa, ana Kira a Kore Su
- Ƙungiyar CNPP ta bukaci a kori manyan jami'an gwamnatin tarayya bayan abin kunya na ma'aikatar bogi da aka ce an samu a Najeriya
- Hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council ta samu kudi har N1.3bn a kasafin kudin 2026 duk da cewa ta bogi ce
- bugu da kari CNPP ta yi gargadi cewa gwamnati ba ta da ikon soke dokar da ta gabatar da ita da kanta ta hanyar sanarwa ga 'yan jarida kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaduna - Ƙungiyar siyasa da aka sani da CNPP ta fito da sanarwa mai tsanani, tana neman a kori manyan jami'an da ke aiki a gwamnatin Bola Tinubu bayan abin kunya na wata ma'aikatar bogi da aka kafa.
Rahoto ya nuna cewa ataimakin sakataren yada labaran ƙungiyar, Kwamrad James Ezema ne ya gabatar da sanarwar a birnin Kaduna.

Source: Facebook
The Guardian ta rahoto ya ce ba a taɓa ganin abin kunya kamar wannan a tarihin dimokuradiyyar Najeriya ba, inda ya zargi gwamnatin APC da rashin iya aiki da gurɓataccen sarrafa lamarin.
Ma'aikatar bogi da aka samu
Labarin ya samo asali ne daga wani mutum mai suna Prince Adeniyi Adeyemi Matthew, wanda ake zargi ya shafe watanni da yawa yana aiki a matsayin Darakta-Janar na wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council.
A cewar CNPP, wannan mutum ya yi amfani da ofis a cikin a Abuja, ya gudanar da tarurruka tare da jakadun ƙasashen waje, kuma ya buɗe asusun banki har da na Babban Bankin Najeriya, duk ƙarƙashin tutar wannan hukuma.
Sai dai Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta karyata cewa yana da asusun banki a CBN bayan ta ce yana da shi a karon farko.
Abin da ya kara rikitar da lamarin shi ne an saka wannan hukuma a cikin kasafin kudin tarayya na shekarar 2026 tare da ba ta fiye da naira biliyan 1.3, ciki har da kuɗin albashi, alawus-alawus da kuma shirin gudanar da taron zuba hannun jari a duniya.

Kara karanta wannan
Rahoton WFP: ADC ta zargi Tinubu da jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a jihohin Arewa 9
Gardadin da aka yi kan soke doka
Ezema ya jaddada cewa kasafin kuɗi ba ya rubuta kansa, kuma kowane ɓangare da ke cikinsa yana wucewa ta hanyar ma'aikatun gwamnati da shugaban ƙasa da kansa.
A ganin CNPP, ba shi yiwuwa gwamnati ta sanya hannu a dokar kasafin kuɗi da ke ɗauke da sunan hukuma, sannan ta fito da sanarwa tana cewa wannan hukuma ta bogi ce.

Source: Facebook
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta hanyar da shugaba Tinubu ya rattaba hannu a wannan doka, hukumar ta sami matsayi na doka har sai majalisar dokoki ta yi amfani da ikon da ta ke da shi ta canza ko soke wannan tanadi.
Maganar korar jami'an Tinubu
CNPP ta kara da cewa idan Najeriya na son ƙasashen duniya su mutunta ta a matsayin ƙasa mai cikakken tsarin mulki, dole manyan jami'an gwamnati da wannan lamari ya shafa su yi murabus ko a kore su nan take tana jiran bincike.
Wannan kira ya zo ne bayan ma ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi ya fito baya-bayan nan ya nemi Tinubu ya yi murabus sakamakon wannan abin kunya.
Gbaja ya yi barazanar zuwa kotu
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya yi barazanar zuwa kotu kan alaƙanta shi da ma'aikatar bogi da aka yi.
Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa ba shi da alaka da zarge-zargen da shugaban hukumar bogin ya masa kan cewa ya nemi kudi a wajensa.
Hakan na zuwa ne bayan fadar shugaban kasa ta nesanta kanta daga ma'aikatar da aka ce an kirkiro ba tare da sanin shugaba Bola Tinubu ba.
Asali: Legit.ng

