A Ba Su Wuta: Gwamnan Bauchi Ya Umarci Sojoji a Shafe 'Yan Bindiga
- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya shaida wa jami'an sojoji cewa za su samu hadin kai domin a shafe yan bindiga da ke damun jama'a
- Ya ce haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara ta'azzarar rashin tsaro kuma wannan ba zai sa a yi sakaci da rayuka ba
- Gwamnan ya ce ko ɗansa ne ke da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa doka ba, a kama shi, sannan a yi masa hukunci dai-dai da laifin da aka tabbatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya umarci dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Safe Haven/Operation Enduring Peace da su ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri.
Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wa aikinsu, tare da tabbatar da cewa babu wani mai aikata laifi da zai tsira daga hukunci a jihar.

Source: Facebook
A ruwayar jaridar Punch, gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata 4 ga watan Agusta, 2026 yayin da ya karɓi sabon Babban Kwamandan Runduna ta 3 ta Sojojin Najeriya da ke Jos, kuma kwamandan Operation Safe Haven/Operation Enduring Peace, Manjo Janar Maxwell Dangana.
Gwamnan Bauchi ya magantu kan rashin tsaro
Daily Post ta wallafa cewa Bala Mohammed ya ce jihar Bauchi ba za ta zuba ido rashin tsaro ya yi kwari ko hana su zaman lafiya ba.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa jami'an tsaro cikakken goyon baya wajen yaƙi da rashin tsaro da tabbatar da dan hukunta masu laifi
Gwamnan ya bayyana cewa haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba na daga cikin manyan abubuwan da ke ɗaukar nauyin ta'addanci da rashin tsaro a jihar.
Sanata Bala Muhammad ya yi gargadin cewa ƙungiyoyin masu aikata laifi na amfani da wannan harkar wajen samun kuɗaɗen da suke ɗaukar nauyin tashe-tashen hankula a yankunan karkara.
Gwamnan Bauchi ya yabi sojoji
Gwamnan ya yabawa rundunar sojin Najeriya bisa jajircewar da take yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma, yana mai cewa jami'an soji sun cancanci yabo maimakon suka saboda sadaukarwar da suke yi wajen barin iyalansu domin kare sauran 'yan ƙasa.
Ya kuma nuna damuwarsa cewa 'yan bindiga da masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba na barazana ga samar da abinci da tattalin arzikin jihar ta hanyar kai hare-hare kan al'ummomi da hana manoma zuwa gonakinsu.

Source: Facebook
A cewarsa, haɗin gwiwa tsakanin jihohin da ke da iyaka da juna zai taimaka wajen murƙushe 'yan bindiga da kuma rusa ƙungiyoyin masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da ke ɗaukar nauyin rashin tsaro.
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa wasu masu ruwa da tsaki na cikin gida suna haɗa kai da masu haƙar ma'adinai ba bisa doka ba saboda ribar kuɗi da suke samu.
Ya ce:
"Ku ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri. Kada ku tausaya wa kowa. Ko da ɗana ne ke da hannu a haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, ku hukunta shi ba tare da wata-wata ba."
A nasa jawabin, Manjo Janar Maxwell Dangana ya ce ziyararsa ta Bauchi na cikin rangadin da yake yi domin sanin halin da yankunan da ke ƙarƙashin jagorancinsa suke ciki bayan karɓar ragamar jagorancin Operation Safe Haven da Operation Enduring Peace makonni biyu da suka gabata.
An yi gano gaskiya kan sadaki a Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Bauchi ta musanta rahoton da ke cewa Gwamna Bala Mohammed ya amince da sadakin N1,500 ga matan da aka saki, wato zawarawa a fadin jihar.
Kwamishina Muhammad Binni ya ce bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ƙarya ce da aka ƙirƙira domin yaudarar jama'a da jefa rudani a cikin maganar sadakin auren matan da suka rabu da mazajensu.
Da ta ke gargadin jama'a, Gwamnati jihar ta bukaci jama'a su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yaɗa su domin kaucewa yada karya da kuma samar da zaman lafiya a fadin Bauchi.
Asali: Legit.ng


