Komai zai Fito: APC na Shirin Fitar da Bayanan Mataimakin Tinubu a 2027

Komai zai Fito: APC na Shirin Fitar da Bayanan Mataimakin Tinubu a 2027

  • Wani babban mamba na kwamitin NWC na jam'iyyar APC ya tabbatar da cewa jam'iyyar ta kai matakin ƙarshe na daura bayanan 'yan takararta a shafin hukumar INEC
  • Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran APC za ta daura bayanan shugaba Bola Tinubu da mataimakin da zai yi takara da shi zuwa tsakiyar wannan makon da muka shiga
  • An riga an daura bayanan gwamnoni huɗu masu ci a kan mulki a shafin INEC yayin da APC ke nazari kan sama da ƙorafe-ƙorafe 700 daga mambobinta da ba su gamsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta ce tana kan hanya wajen miƙa sunayen 'yan takararta na shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ta tarayya ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kafin wa'adin ranar 11 ga Yuli, 2027.

Kara karanta wannan

Umarnin da fadar shugaban kasa ta ba DSS, EFCC kan batun ma'aikatar bogi

Wani babban mamba na kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam'iyyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa aikin daura bayanan ya yi nisa sosai.

Shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima
Bola Tinubu da Kashim Shettima a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Za a sanar da mataimakin Tinubu

The Nation ta rahoto cewa majiyar ta ce ana sa ran daura bayanan shugaba Bola Ahmed Tinubu da na mataimakinsa zuwa shafin INEC kafin tsakiyar wannan mako.

Legit ta rahoto ya ce:

"Muna ci gaba da daura bayanan 'yan takararmu na majalisar dokoki ta kasa ba tare da wata matsala ba.
"Muna fatan cewa nan da ko kafin ranar Laraba mai zuwa za mu daura bayanan shugaba Bola Ahmed Tinubu da na mataimakinsa. Muna da cikakken tabbacin cewa za mu cika wa'adin ranar 11 ga Yuli wajen daura bayanan dukkan 'yan takararmu a shafin INEC."

Aikin da APC ke yi a yanzu

Binciken da aka gudanar ranar Lahadi a sashen fasahar sadarwa (ICT) na jam'iyyar da ke hedikwatar Muhammadu Buhari House a Abuja ya nuna cewa ƙungiyar masu fasaha ta ci gaba da samun damar shiga shafin INEC ba tare da tangarda ba.

Kara karanta wannan

INEC ta kirkiro shafin rajistar katin zabe ta yanar gizo, ta kara wa'adin mako 2

Majiyoyi daga sashen sun bayyana cewa an riga an daura bayanan mafi yawan manyan shugabannin majalisar dokoki ta tarayya ta 10 da kuma wasu daga cikin 'yan majalisar da ke kan kujerunsu.

Shugaban APC na kasa a wajen taro
Shugaban APC, Farfesa Yilwatda Nentawe. Hoto: All Progress Congress
Source: Facebook

Haka kuma, an yi nasarar daura bayanan gwamnoni huɗu masu ci a kan mulki, wato AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, Mai Mala Buni na Jihar Yobe, Hope Uzodimma na Jihar Imo da Dapo Abiodun na Jihar Ogun.

Punch ta wallafa cewa a halin yanzu jam'iyyun siyasa a Najeriya na kokarin kammala shirye-shiryen daura bayanan 'yan takararsu kafin lokaci ya kure.

'Yan takarar da aka sauya

A wani rahoton, kun ji cewa APC ta cire 'yan takarar Sanata shida da kuma 'yan takarar majalisar wakilai 19 bayan zaɓen fitar da gwani na watan Mayun 2026.

Legit Hausa ta rahoto cewa mazabun da abin ya shafa sun haɗa da jihohin Abia, Kogi, Taraba, Benue, Ebonyi, Ondo, Kaduna, Neja da Kwara.

Daga bisani, an aika sabon jerin sunayen ga INEC ta wata wasiƙa da shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da sakataren jam'iyyar na kasa, Ajibola Basiru, suka sanya wa hannu tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng