Yadda Shugaban Ma'aikatar Bogi Ya Rika Tarurruka da Manyan Jami'an Gwamnatin Tinubu

Yadda Shugaban Ma'aikatar Bogi Ya Rika Tarurruka da Manyan Jami'an Gwamnatin Tinubu

  • Fadar shugaban kasa ta fito ta bayyana cewa ba ta san da zaman hukumar Adeyemi Adeyemi, ya yi ikirarin yana jagoranta ba
  • Shugaban hukumar ya rika gudanar da tarurruka da manyan jami'an gwamnati ciki har da Ministoci da shugaban hukumar EFCC
  • Tun da farko shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya fara fitowa ya bayyana cewa ba a san da zaman hukumar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Adeniyi Adeyemi, mai kiran kansa shugaban hukumar bunkasa tallafin kasashen waje ta fadar shugaban kasa, ya gudanar da tarurruka da jami'an diflomasiyya da manyan jami'an gwamnati tare da daukar hotuna.

Adeyemi ya rika yin hakan ne kafin Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar Shugaba Bola Tinubu, ya fitar da sanarwar cewa ba a san da hukumar ba a watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Yadda aka kafa mai'akatar bogi a Najeriya ba tare da Tinubu ya gano ba

Adeyemi ya gana da Benjamin Kalu
Adeniyi Adeyemi tare da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu Hoto: Adeniye Adeyemi Matthew
Source: Facebook

The Cable ta ce Gbajabiamila ya kawo karshen lamarin ne a ranar 11 ga watan Yuni, inda ya bayyana nada Adeyemi a matsayin shugaban hukumar a matsayin abin da ba shi da tushe kuma na yaudara.

An musanta wanzuwar ma'aikatar Adeyemi

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 1 ga watan Yulin 2026 a shafin Facebook, Bayo Onanuga, ya goyi bayan tsohon shugaban majalisar wakilan, inda ya bayyana hukumar ta Adeyemi a matsayin ta bogi kuma wadda gwamnatin tarayya ba ta san da ita ba.

An ruwaito cewa Adeyemi ya gudanar da ayyukan wannan hukuma ta bogi ne daga tsakiya zuwa karshen shekarar 2025, lokacin da ya gudanar da tarurruka da wakilai da manyan jami'an gwamnati daga babbar sakatariyar tarayya da ke Abuja.

Yadda ya rika ganawa da manya

A watan Yulin 2025, Adeyemi ya gana da Benjamin Kalu, mataimakin shugaban majalisar wakilai, a zaman wani bangare na kokarin daidaita muradin manufofi da kudurin majalisa.

Kara karanta wannan

DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya

A cewar jaridar Punch, an gudanar da taron ne a ofishin mataimakin shugaban majalisar da ke majalisar dokoki ta kasa.

Haka zalika, a watan Satumban 2025, Adeyemi ya gana da Ola Olukoyede, shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC).

A cewar jaridar The Nation, taron, wanda aka gudanar a babban ofishin EFCC da ke Abuja, yana cikin kokarin zurfafa hadin gwiwa domin karfafa yunkurin Najeriya na janyo masu zuba hannun jarin kasashen waje.

Adeyemi ya gana da shugaban hukumar EFCC
Adeniyi Adeyemi tare da shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Adeyemi ya yi taro da Ministoci

Tsakanin watan Yuni da Satumba na shekarar da ta gabata, Adeyemi ya kuma gudanar da jerin tarurruka da jami'an diflomasiyya da ministocin Najeriya.

A watan Agusta, ya gana da Suwaiba Ahmad, karamar Ministar ilimi, da Yusuf Sununu, karamin Ministan ayyukan jin kai da rage radadin talauci, domin karfafa shirye-shiryen gwamnati na rage talauci da ilimi.

A cikin wannan watan ne kuma ya tattauna da Thirapath Mongkolnavin na ofishin jakadancin Thailand, da Matthawut Malisuwan, mataimakin shugaban tawagar jakadanci, a zaman wani bangare na kokarin bunkasa zuba jarin kasashen waje a Najeriya.

Kara karanta wannan

Amupitan: Shugaban INEC ya dauko batun satar akwatin zabe da magudi gabanin 2027

An bukaci Tinubu ya kori Gbajabiamila

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya tsoma baki a zargin Femi Gbajabiamila ya karbi na goro.

Atiku ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da shugaban ma'aikatan na fadar shugaban kasa, bisa zargin karɓar Naira miliyan 400.

Hakazalika, Atiku ya ce ya kamata Tinubu ya jagoranci gwamnati ta hanyar tabbatar da cewa duk jami'ansa suna fuskantar hukunci idan aka samu zarge-zargen cin hanci ko rashin gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng