Karfin Hali: Yadda aka Kama Mutum 2 da Zargin Cefanar da Filayen Gwamnatin Kano
- Wadansu mutane da suka yi karfin hali sun shiga matsaloli bayan an kama su da zargin sayar da kadadorin gwamnatin jihar Kano kai tsaye
- Tuni aka baza jami'ai, aka kuma yi nasara cafke su bayan an zurfafa bincike a kokarin da ake yi na dakile cefanar da filayen gwamnati
- Kafin an cafke su, an gano yadda suka sauya wurin domin su ci gaba da haramtacciyar sana'ar da su ke yi na cinikin filayen gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta kama wasu mutum biyu bisa zargin rabawa da sayar da filayen gwamnati ba bisa ka'ida ba a yankin Rimin Zakara da ke ƙaramar hukumar Ungogo.
Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane na jihar, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano.

Source: Facebook
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan ya ce mutanen da aka kama na daga cikin waɗanda ake zargi da mamaye filayen gwamnati tare da sayar da su ba bisa ƙa'ida ba.
Gwamnatin Kano ta dauki mataki
Kafar Muhasa ta wallafa a shafin Facebook cewa Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce gwamantin Kano ta yi kokari wajen kawo ƙarshen rikicin filaye a Rimin Zakara.
Sai dai an sam wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun koma yankin Gundutse da ke ƙaramar hukumar Kura, inda suka ci gaba da gudanar da haramtacciyar hada-hadar filaye.

Source: Original
Kwamishinan ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da Muhammad Kabir, mai shekaru 57 daga unguwar Gaida, da Kamilu Iliyasu, mai shekaru 55 daga yankin Zoo Road.
Ya ƙara da cewa jami'an tsaro na ci gaba da neman wani da ake zargi mai suna Mustapha Matazu, wanda ake kyautata zaton ya tsere.
Gwamnatin Kano ta yi Allah wadai
Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya yi Allah wadai da ci gaba da mamayewa da sayar da filayen gwamnati ba bisa ƙa'ida ba da wasu ke yi.
Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kano ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kamo tare da gurfanar da duk masu hannu a irin waɗannan ayyuka.
Ya kuma shawarci jama'a da su riƙa tabbatar da sahihancin mallakar duk wani fili kafin su saya ta hanyar tuntuɓar Ma'aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane ta jihar.
Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce yin hakan zai taimaka wa masu saye su guje wa fadawa hannun masu damfara da kuma asarar kuɗaɗensu.
Yan kasuwa sun tuna alkawarin gwamnati
A baya, mun kawo labarin cewa 'yan kasuwar Kano da iftila'in gobara ya shafa sun tunatar da gwamnatin tarayya alkawarin da ta yi na tallafa masu da kudi bayan konewar kadarorinsu kurmus.
Wasu daga cikin yan kasuwar da su ka wakilci sauran sun yi tattaki kafa da kafa inda su ka tattauna da babba a gwamnatin Bola Tinubu Gwamnatin Tarayya, wato sakataren gwamnati, George Akume.
A lokacin da aka yi gobarar watanni biyar da su ka gabata, Gwamnatin Tarayya ta aika tawaga inda ta jajantawa yan kasuwa da al'ummar jihar Kano, tare da yi masu alkawarin N5bn domin su rage zafi.
Asali: Legit.ng

