Dara Ta ci Gida: Wani Bam Ya Fashe da Ƴan Ƙungiyar ISWAP yayin da Suke Hada Shi

Dara Ta ci Gida: Wani Bam Ya Fashe da Ƴan Ƙungiyar ISWAP yayin da Suke Hada Shi

  • Mutane biyar da ake zargin mayaƙan ISWAP ne sun mutu bayan wani shirin hada bam da suke yi a jihar Borno
  • Rahotanni sun ce Usman Dan Fulani tare da ƙwararrun masu ƙera bama-bamai biyu daga ƙasashen waje da wasu biyu sun mutu
  • Majiyoyin tsaro sun ce sojoji sun ƙara sintiri da farmaki a Monguno, Marte da Gamboru Ngala domin hana ISWAP sake haɗuwa da ƙarfafa hare-harensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Wasu mayakan ƙungiyar ISWAP biyar ne sun mutu sakamakon tashin wani abin fashewa a jihar Borno.

Lamarin ya auku ne yayin da suke haɗa na'urorin fashewa na zamani (IED) a ƙauyen Maina Daya da ke ƙaramar hukumar Marte a Borno.

Yan ISWAP 5 sun mutu a Borno
Taswirar jihar Borno da ke fama da hare-haren ta'addanci. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Zagazola Makama, wata kafar da ke mayar da hankali kan yaƙi da ta'addanci a yankin Tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

An kashe dan siyasa da 'yan bindiga suka kai kazamin hari Filato da dare

Kauyen da fashewar bam ta kashe ƴan ISWAP

Majiyoyi suka ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Maina Daya, tsakanin Sabon Tumbu da Jubilaram, mai nisan kusan kilomita 29 gabashin Monguno.

Rahoton ya ce, bisa bayanan da aka samu daga majiyoyin tsaro, Usman Dan Fulani, wanda ake zargin jami'in kula da lafiya na ISWAP ne, yana cikin waɗanda suka mutu sakamakon fashewar.

Majiyoyin sun kuma bayyana cewa ƙwararrun masu ƙera na'urorin fashewa guda biyu daga ƙasashen waje da wasu mutane biyu da ake zargin ƙwararrun masu haɗa bama-bamai na ISWAP ne sun rasa rayukansu.

An ce waɗannan da ake zargi suna shirya na'urorin fashewar ne domin kai hare-hare lokacin da fashewar ta faru ba tare da shiri ba.

Majiyoyin tsaro sun ce wannan na nuna cewa ƙungiyar na iya kasancewa tana shirin kai hare-hare a manyan hanyoyin da sojoji ke amfani da su wajen kai kayayyaki a yankin Sector 1 na Operation HADIN KAI.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun saki sunayen mutane 2 da ke ba 'yan bindiga bayanai a Bauchi

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa mutuwar waɗannan ƙwararrun masu ƙera bama-bamai na iya rage ƙarfin ISWAP na kai hare-haren bama-baman gefen hanya a hanyar Marte zuwa Monguno na ɗan lokaci.

Haka kuma, majiyoyin soji sun ce an umarci dakaru su ƙara sintiri, gudanar da bincike da kewaye, tare da kai hare-hare na musamman a yankunan Monguno, Marte da Gamboru Ngala.

Rahoton ya ƙara da cewa waɗannan matakan na da nufin hana ƙungiyar ta'addancin sake haɗuwa ko kuma sake gina ƙarfin ta wajen ƙera na'urorin fashewa.

Rahoton ya ƙara da cewa waɗannan matakan na da nufin hana ƙungiyar ta'addancin sake haɗuwa ko kuma sake gina ƙarfin ta wajen ƙera na'urorin fashewa.

Ƙarin bayani na tafe ....

An bankado shirin Boko Haram a Najeriya

Mun ba ku labarin cewa hukumar DSS ta yi gargadin cewa ‘yan Boko Haram na shirin kai manyan hare-hare a ƙananan hukumomin Michika da Askira-Uba.

Rahoton ya ce ‘yan ta’addan na shirin yin garkuwa da manyan jami’an gwamnati, hakimai, fastoci da mazauna yankunan.

DSS ta buƙaci jami’an tsaro da masu gadin dazuka su ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana hare-haren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.