Bayani kan Ƙarin Albashi da Tinubu Ya Yi wa Ƙanana da Manyan Sojojin Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin albashin jami'an rundunar sojin Najeriya daga kashi 30 zuwa 80 cikin 100, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumba
- Sabon tsarin albashin zai amfani kusan sojoji 250,000, yayin da jimillar kuɗin albashi na shekara za ta ƙaru daga Naira biliyan 660 zuwa biliyan 924
- Fadar shugaban ƙasa ta ce an yi ƙarin albashin ne domin yabawa sadaukarwar sojoji wajen yaƙi da ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin albashin jami'an rundunar sojin Najeriya tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100, domin inganta walwalarsu da ƙarfafa gwiwarsu wajen gudanar da ayyukan tsaro.
Sabon tsarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, kuma ana sa ran kusan jami'ai da sojoji 250,000 za su amfana da shi.

Kara karanta wannan
2027: Yadda Tinubu, Atiku da sauran ƴan takara ke shirin amfani da tsofaffin gwamnoni

Source: Twitter
Tinubu ya karawa sojoji albashi
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a shafinsa na X.
A cewar sanarwar, manyan jami'ai daga mukamin Kanar zuwa Janar za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin 100.
Jami'an da ke tsakanin mukamin Kanar zuwa Warrant Officer kuma za su samu ƙarin albashi na kashi 50 cikin 100.
Haka kuma, sojoji daga mukamin Private zuwa Staff Sergeant za su amfana da mafi girman ƙarin albashi, wanda ya kai kashi 80 cikin 100.
Sabon tsarin zai ƙara yawan kuɗin albashin rundunar sojin Najeriya na shekara daga Naira biliyan 660 zuwa Naira biliyan 924.
Dalilin ƙarin albashin
Bayo Onanuga ya ce shugaban ƙasa ya amince da ƙarin albashin ne domin nuna godiya ga jajircewa da sadaukarwar jami'an rundunar soji wajen yaƙi da 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma 'yan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Ya nakalto Shugaba Tinubu yana cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da fifiko ga walwalar sojoji tare da samar musu da makamai da kayan fasaha na zamani domin sauƙaƙa musu gudanar da aikinsu.
Shugaban ya ƙara da cewa babu wata ƙasa da za ta samu ci gaba ba tare da tsaro ba, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da dukkanin ƙarfin hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.

Source: Getty Images
Tinubu ya kuma buƙaci jami'an rundunar sojin Najeriya su ɗauki wannan mataki a matsayin alamar godiya da girmamawa ga irin hidimar da suke yi wa ƙasa, yana mai bayyana cewa haɗin kai zai taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar Najeriya.
An yi wa sojoji karin albashi
Tun da fari, mun ruwaito cewa, ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya ce mafi karancin albashin soja yanzu ya kai N100,000 duk wata.
Janar Christopher Musa ya ce har yanzu kasafin da ake warewa fannin tsaro ba ha wadatarwa kamar yadda ya kamata.
Ministan ya kuma musanta rahoton cewa ba a bai wa sojoji ingantacen abinci, yana mai cewa zargin da ake ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng
