Abu ya Girma: Shugaba Tinubu Ya ba ICPC Umarni kan Ma'aikatar Bogi
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba ICPC umarnin bincike kan wata cibiyar gwamnati ta karya da ake kira PFIPC da ake ta cece-kuce a kanta
- Wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya kira kansa a matsayin shugaban hukumar, inda ya ce shugaban kasa ne ya nada shi
- Shugaba Tinubu ya bai wa hukumar ICPC kwanaki 30 domin kammala bincike tare da gabatar da cikakken rahoto a gare shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarni ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan hukumar PFIPC.
Shugaba Tinubu ya umarci cewa a kammala binciken sannan a mika masa cikakken rahoto a kai a cikin tsawon kwanaki 30.

Kara karanta wannan
Tinubu ya waiwayi manyan kamfanonin kafafen sadarwa, za a binciki Meta, X da sauransu

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X a ranar Talata, 7 ga watan Yulin 2026.
Bola Tinubu ya umarci a binciki PFIPC
Wannan umarni ya biyo bayan gano wata hukuma ta bogi ta PFIPC, wadda gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta taba kafa ta ba, kuma ba ta da wani tushe a cikin kowace doka, amincewar majalisar zartarwa.
Wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya bayyana kansa a matsayin shugaban wannan hukuma da ake kira PFIPC, kuma ya yi ikirarin karya cewa shugaban kasa ne ya nada shi.
Wadanne abubuwa ICPC za ta bincika?
Daga cikin batutuwan da ICPC za ta bincika har da wasikun nadin mukami na jabu da sauran takardun gwamnati amfani da ikirarin karya na nadin shugaban kasa domin nema ko samun amincewa ta hukuma da goyon bayan diflomasiyya, gami da sauƙaƙa samun biza; da kuma bude asusun banki da dama da sunayen hukumomin gwamnati na bogi ta hanyar amfani da takardun da ake zargin na jabu ne.
Shugaba Tinubu ya umarci ICPC da kada kawai ta binciki abubuwan babban wanda ake zargi sauran abokan huldarsa suka yi ba, har da yanayin da ka iya ba wa wannan hukuma damar samun yin abubuwan da ta yi wadanda suka nuna kamar halastacciya ce.
Za a hukunta wadanda aka samu da laifi
Tinubu ya jaddada cewa dole ne a kare martabar fadar shugaban kasa da kuma cibiyoyin gwamnatin tarayya daga kowane irin ƙoƙarin yin karya ko amfani da sunan gwamnati ba bisa ka'ida ba.
"Shugaban kasa ya umarci cewa dukkan mutanen da aka samu da laifi a hukunta su daidai da tanadin doka."
Bayo Onanuga

Source: Twitter
Gbajabiamila ya yi barazanar kai Adeyemi kara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar kai shugaban ma'aikatar bogi, Adeniyi Adeyemi, kara gaban kotu.
Femi Gbajabiamila ya yi barazanar ne biyo bayan zarge-zargen da suka danganta shi da kisan kai, karbar cin hanci, da sauran ayyukan laifi.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ya bukaci Adeyemi da ya goge dukkan bayanai, da suka hada da rubuce-rubuce, bidiyoyi, da muryoyin da aka nada.
Asali: Legit.ng
