Kano: Halin da Kadarorin Malami ke ciki bayan Kotu Ta Kwace saboda Almundahana

Kano: Halin da Kadarorin Malami ke ciki bayan Kotu Ta Kwace saboda Almundahana

  • Kotu ta tabbatar da kwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon Ministan shari'a Abubakar Malami, yayin da ta saki tara daga cikinsu
  • Gidan da ke Ahmadu Bello Way a Kano ya zama kufai bayan EFCC ta karbe shi, amma an gano wata kadarar 'dan takarar gwamnan na aiki
  • Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzki zagon kasa ta EFCC ta ce duk wasu kadarorin da ba ta karbe su ba tukuna ana ci gaba karya doka a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kotun Tarayya ta tabbatar da kwace wasu kadarori da ake dangantawa da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami.

An kwace wadannan manyan kadarori ne bayan ta yanke hukuncin cewa masu ikirarin mallakarsu sun kasa tabbatar da cewa sun samo su ne ta hanyar da ta dace.

Kara karanta wannan

Dan majalisar PDP ya san makomarsa da aka kai shi gaban kotu bayan barin APC

An kwace da yawa daga cikin kadarorin Malami
Abubakar Malami dan takarar gwamnan ADC a jihar Kebbi Hoto; Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito yadda Alkalin kotun, Joyce Abdulmalik, ta amince da bukatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), inda ta ce Malami da sauran masu neman a mayar masu da kadarorin ba su gabatar da isassun hujjojin da ke nuna sun mallake su bisa doka ba.

Malami: Yadda aka yi hukuncin kotu

Labarin da ya kebanta da Premium Times ya ce sai dai kotun ta saki kadarori tara daga cikin kadarori 57 da EFCC ta nemi a kwace gaba daya, bayan ta ce hukumar ba ta tabbatar da cewa an same su ta haramtacciyar hanya ba.

EFCC ta shigar da karar kwace kadarorin ne tun watan Janairu, 2026 tana zargin cewa Malami ya mallake su da kudaden da aka samu ta haramtacciyar hanya a lokacin da yake rike da mukamin Babban Lauyan Tarayya tsakanin shekarun 2015 zuwa 2023.

Malami tare da mutum 14, ciki har da iyalansa da kamfanoninsa da otal-otal da jami'arsa, sun kalubalanci umarnin kotun na wucin gadi, suna masu cewa sun mallaki kadarorin ne bisa ka'ida.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano inda aka boye gawar shugaban al'umma da aka hallaka a Imo

An hango ana aiki a kadarar Malami

A lokacin da aka kai ziyara Zeenoor Hotels Ltd da ke Kano, an tarar da otal din na ci gaba da karbar baki kamar yadda aka saba.

An gano kadarorin Malami na Kano da aka kwace
Daya daga cikin kadarorin Malami, tambarin EFCC Hoto: EFCC
Source: Twitter

Sai dai jami'an karbar baki sun ki yin karin bayani kan hukuncin kotun, inda daya daga cikinsu ya ce abin da zai iya tabbatarwa kawai shi ne cewa otal din na ci gaba da aiki.

Wani jami'in tsaro da ke bakin kofar otal din ya bayyana cewa an sanar da su cewa jami'an gwamnati za su zo domin karbe wurin bayan hukuncin kotu.

A daya bangaren kuma, gidan da ke lamba ta 9, Ahmadu Bello Way, wanda ke kusa da Gidan Gwamnatin Kano, ya zama kufai.

Jami'an tsaron yankin sun ce babu kowa a cikin gidan, yayin da jami'an 'yan sanda masu sulke ke gadinsa. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce hukumar ta fara karbar kadarorin da kotu ta ba da umarnin a kwace.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta yanke hukunci kan amaryar da ta kashe mijinta kwanaki 9 da aurensu

Ya kara da cewa EFCC ta riga ta karbe gidan da ke Ahmadu Bello Way, yayin da za a ci gaba da karbar sauran kadarorin da hukuncin kotun ya shafa a hankali.

Malami ya zabi abokin takara

A wani labarin, mun wallafa cewa Abubakar Malami ya zaɓi Musa Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan Kebbi na jam'iyyar ADC domin zaɓen 2027 da ke kara kusantowa.

Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar Zagi zai sauke nauyin da aka ɗaura masa idan suka samu nasara a zaɓen da APC da sauran jam'iyyu suka ci alwashi a kai.

Naɗin ya zo ne kwanaki bayan wata kotun tarayya ta ba da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake dangantawa da tsohon AGF, Abubakar Malami, wadanda ake zargin ya samu ta barauniyar hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng