Yan Sanda Sun Cafke Mahaifin wanda Ya Kafa Ma'aikatar Bogi a Gwamnatin Tinubu

Yan Sanda Sun Cafke Mahaifin wanda Ya Kafa Ma'aikatar Bogi a Gwamnatin Tinubu

  • Rahotanni sun bayyana cewa rundunar yan sandan Najeriya ta kama mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi kan binciken da ake yi kan zargin kirkirar hukuma PFIPC
  • Lamarin a fara jawo martani inda lauyan kare hakkin bil'adama, Femi Falana (SAN), ya ce babu wata doka da ta amince da kama dan uwa a madadin wanda ake nema
  • Wannan an zuwa ne a lokacin da Adeyemi ya amsa cewa zai halarci kotu, sannan za a wanke shi kan zargin cewa ya yi gaban kansa wajen kafa hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Lauyan kare hakkin bil'adama, Femi Falana (SAN), ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun kama mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi.

Mr. Adeyemi shi ne mutumin da ake bincike a kansa kan zargin kirkirar wata hukuma da ta samu damar shiga cikin kasafin kasa, PFIPC.

Kara karanta wannan

'Akwai dalili': Rundunar 'yan sanda ta kama motocin mutane fiye da 80 a Kano

An kama mahaifin Adeyemi da ya kafa hukumar bogi a Najeriya
Sufeton yan sandan Najeriya Tunji Disu da Adeniyi Adeyemi a hagunsa Hoto: Nigeria Police Force/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallaaf cewa rahotanni sun ce jami'an 'yan sanda sun kai samame gidan iyalan Adeniyi da ke Ogbomoso a jihar Oyo da safiyar Litinin, 6 ga watan Yuli, 2026 inda suka kama mahaifinsa tare da wani abokin iyali da ya je ziyara.

An kama mahaifin 'shugaban' PFIPC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa rahotanni sun ce mahaifiyar Adeniyi mai shekaru ta shiga cikin firgici bayan kama mijinta, lamarin da ya sa makwabta suka kwashe ta daga gidan domin samun kulawa.

Da yake magana ta wayar tarho, Falana ya ce babu wata doka da ke ba jami'an tsaro damar kama wani mutum saboda zargin da ake yi wa dan uwansa.

Ya ce:

"Jami'an 'yan sanda sun mamaye gidan iyayen Prince Adeyemi Adeniyi da ke Ogbomoso. Sun kama mahaifinsa. Babu wata doka da ta halatta kama mutum a madadin wani. Matashin ya yi alkawarin zai gurfana a gaban kotu, me ya sa za a kama mahaifinsa?"

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

Wasu mazauna yankin da suka nemi a sakaya sunayensu sun tabbatar da faruwar lamarin, suna cewa jami'an sun isa gidan da motoci hudu kafin daga bisani su tafi da mahaifin Adeniyi.

PFIPC: An dimauce kan kama mahaifin Adeyemi

Wani shaidar gani da ido kuma ya ce an kama mahaifin tare da wani mutum da ya zo ziyarar iyalin a wannan safiyar, yayin da aka bar mahaifiyar cikin halin firgici.

Har yanzu yan sanda ba su ce komai a kan Adeyemi ba
Adeyini Adeyemi da ake zargin ya kafa hukumar bogi a Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar 'yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan samamen da aka ce ta kai ba.

Badakalar PFIPC ta ci gaba da daukar hankalin 'yan Najeriya bayan zargin cewa an kafa hukuma sukutum amma ta bogi, duk da ikirarin cewa tana aiki karkashin Fadar Shugaban Kasa.

Yadda hukumar PFIPC ta rika aiki

A baya, mun wallafa cewa fadar shugaban kasa ta fito ta bayyana cewa ba ta san da zaman hukumar Adeyemi Adeyemi, ya yi ikirarin yana jagoranta ba duk da yadda aka ganta a cikin kasafin kudin kasar nan.

Shugaban hukumar ya rika gudanar da taruka da manyan jami'an gwamnati ciki har da Ministoci da shugaban hukumar da wasu daga cikin jami'ai daga kasashen waje da sunan gwamnatin Najeriya

Haka kuma daga cikin wadanda hukumar ta bogi ta zauna da su har da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC kafin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila,ya fasa kwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng