Adeyemi Adeniyi: Abubuwa 7 da Suka Daure Kai game da Shugaban Ma'aikatar Bogi

Adeyemi Adeniyi: Abubuwa 7 da Suka Daure Kai game da Shugaban Ma'aikatar Bogi

Prince Adeyemi Adeniyi Micheal ya shiga tarihi a Najeriya sakamakon zargin shi da aka yi da kafa hukuma ta bogi da ba a san da zamanta ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Sai dai lamarin ya wuce yadda ake tunani, duk da Gwamnatin tarayya ta fitar da jawabi, hakan sai ya kara dumbuza mafi yawan jama’a cikin duhu.

A rahoton nan, Legit Hausa ta tattaro wasu abubuwan sarkakiya game da Prince Adeyemi Adeniyi da kuma hukumomin gwamnati na PFIPC da PEAC.

Adeyemi Adeniyi Micheal
Shugaban PFIPC, Adeyemi Adeniyi Micheal da babban hadimin fadar shugaban kasa Hoto: Demehin Micheal Oluwafemi Loju/Femi Gbajabiamilla
Source: Facebook

PFIPC: Abubuwan tambaya a kan Adeyemi Adeniyi

1. Ta ina hukumar bogi ta shiga kasafin kudi?

Daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali shi ne yadda wannan hukuma da aka ce ta bogi ce, ta samu shiga cikin kasafin kudin 2026.

Bayanan da aka samu daga Sahara Reporters sun tabbatar da cewa har an ware wa wannan hukuma N1.3bn a cikin kundin kasafin kudin bana.

Kara karanta wannan

'A je kotun mana': 'Shugaban' hukumar PFIPC da ake zargin ta bogi ce ya magantu

2. Hukumar tana da adireshi a yanar gizo

Wani matashi da yake kokarin bankado rashin gaskiya a kafar X, Henry Shield ya tabbatar da hukumar tana da adireshin yanar gizo.

Wannan adireshi na yanar gizo ba gama-garin adireshi ba ne, wanda yake karkashin gwamnatin Najeriya ne wato samfurin .gov.ng.

Sai dai zuwa yanzu mun fahimci wannan shafi ya daina aiki, babu da tabbacin ingancinsa kafin nan.

3. ‘Yan majalisar Najeriya sun rika gayyatar Adeyemi

A dandalin X, wani mai suna Imran Wakili ya fito da hotuna da suka nun goron gayyatar da majalisa ta rika aikawa Prince Adeyemi Adeniyi.

Majalisar dattawan Najeriya da Majalisar wakilai ta taba tura wa wannan shugaba na bogi da takardun gayyara zuwa wani taro.

An kuma ga hotunan shi tare da Mataimakin shugaban majalisar wakilai wato Ben Kalu da sunan yana neman hadin kan su wajen aikinsa.

4. Asusun gwamnati a bankin CBN

Kara karanta wannan

NYSC: Surutu yayi yawa minista ya canza magana game da sauyin khaki da adire

Carlo Gambino da yake magana a shafinsa a X, ya yi mamakin yadda hukumar nan ta bude asusu a CBN wanda shi ne babban bankin Najeriya.

Masu nazari a kan harkokin gwamnati, sun ce ba za a bude asusu a bankin CBN ba tare da sahalewar manyan jami’an gwamnatin tarayya.

Ahmad Musa Husseini wanda ya san kan aikin gwamnati, ya yi magana a shafin Facebook yake cewa da alama an yaudari gwamnati a badakalar.

5. Hukumar bogi mai ma’aikata 300

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto na musamman da ya nuna yadda ma’aikatar da ake magana a kai ta dauki mutane har 300 aiki a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta amince a dauki mutane aiki da za su tafiyar da ma’aikatar mai karyar alhakin jawo hannun jari daga kasar waje inji RFI Hausa.

Gwamnatin Najeriya
Wasu jami'an Gwamnatin Najeriya suna taro da Bola Tinubu Hoto: Olusegun Dada
Source: Facebook

6. Adeyemi ya share ofis yana aiki

Dama can an ji ‘dan jarida Ja’afar Ja’afar ya fayyace yadda wanda ake zargin ya samu wuri ha rya bude ofis a sakatariyar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Canji ya tabbata, an bayyana sabon tufafin aikin bautar ƙasa na NYSC a Najeriya

A ofishin na Abuja, an ga yadda yake zama da mutane iri-iri, Legit Hausa a bincikenta, ta lura cewa daga ciki har da jami’an kasahen ketare.

Akwai bidiyoyi daga The Cable da ke nuna wani taro na kasa-da-kasa da Adeyemi ya shirya kwanaki kuma ya samu halartar har da jakadun waje.

7. Hadin guiwar PFIPC da hukumar EFCC

Duk da cewa an bankado wasu abubuwan tambaya tun 2015 game da wannan DG, hotunan shi da manyan jami’an EFCC suna yawo a Najeriya.

EFCC ce hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, amma har can Adeyemi ya je aka zauna da shi a bara.

Wasu bayanai da aka yi sun nuna cewa hukumarsa ta hada-kai ne da EFCC, akasin tunanin da ake yi cewa ya je ya amsa wasu tambayoyi.

Ma'aikatar bogi: Shugaban hukuma ya wanke kan shi

Wani rahoto da aka samu ya ce shugaban hukumar bogi ta PFIPC, Adeniyi Adeyemi ya ce lamarin zargin da ake yi kansa ya riga ya kai gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yadda aka kafa mai'akatar bogi a Najeriya ba tare da Tinubu ya gano ba

Adeniyi Adeyemi ya nuna kwarin gwiwarsa cewa za a wanke shi daga zarge-zargen a shari'ar da za a yi domin kuwa nada shi aka yi a wannan mukami.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wannan mutumi ɗan damfara ne, tana zarginsa da ƙirƙirar hukuma, jabun takardu da buɗe asusun banki a CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng