Shugaban EFCC Ya Samu Sako Mai Zafi bayan Rufe Asusun Gwamnatin Osun
- Gwamna Ademola Adeleke ya bukaci shugaban hukumar EFCC ya bayyana dalilin rufe asusun gwamnatin jihar Osun
- Adeleke ya ce an dauki matakin ne ba tare da umarnin kotu ba, yana mai bayyana hakan a matsayin barazana ga dimokuradiyya
- Gwamnatin Osun ta ce za ta shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Osogbo domin kalubalantar matakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Osogbo, Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kalubalanci shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede.
Gwamna Adeleke ya kalubalanci Olukoyede ya bayyana dalilin da ya sa aka bayar da umarnin rufe asusun gwamnatin jihar Osun.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Adeleke ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Osun ranar Laraba, 5 ga watan Agustan 2026.
Gwamna Adeleke ya bayyana matakin a matsayin abin da ya saba wa doka, yana mai cewa hakan na mayar da dimokuradiyyar Najeriya abin dariya.
Gwamna Adeleke ya yi zarge-zarge
Gwamnan ya ce hukumar EFCC ta dauki matakin ne ba tare da samun umarnin kotu ba, yana mai jaddada cewa ba za su amince da hakan ba.
“Dukkan wadannan tsoratarwa da hare-hare an yi su ne bisa umarnin Gboyega Oyetola kan wani zabe da dan takararsa ba zai iya lashewa ba.”
“Kamar dai wadannan ba su isa ba, a safiyar yau mun karbi wasika daga bankinmu, wadda ta zo tare da wata wasika daga EFCC mai umartar bankin da ya rufe asusun gwamnatin jihar Osun.”
“An dauki wannan mataki ba tare da umarnin kotu ba. Ya kamata mu kasance a cikin dimokuradiyya inda doka za ta rika yin tasiri a kowane lokaci. Saboda haka, ba za mu amince da hukumomin tarayya su take hakkin da kundin tsarin mulki ya bai wa gwamnatocin jihohi ba.”
“Wannan barazana ce ga dimokuradiyyarmu. Idan muka yi shiru muka kyale wannan saba doka, nan ba da dadewa ba abin da ya rage na dimokuradiyyarmu zai salwanta gaba daya."
"Abin da nake bukata shi ne shugaban EFCC ya bayyana wa mutanen kirki na jihar Osun da ‘yan Najeriya gaba daya dalilin da ya sa ya rufe asusun gwamnatin jihar Osun, sannan ya gabatar da hujjar da za ta tabbatar da dalilin da zai bayar.”
“Wannan da sauran abubuwan da suka saba wa doka da ake yi wa jihar Osun suna mayar da dimokuradiyyarmu abin dariya. Na umarci Antoni Janar na jihar ya kalubalanci wannan saba doka a babbar kotun tarayya da ke Osogbo.”
- Gwamna Ademola Adeleke
Adeleke ya yi bayani
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan ko EFCC ta gayyaci jami’an gwamnatin jihar domin yi musu tambayoyi kafin rufe asusun, Adeleke ya ce hukumar ta gayyaci jami’an gwamnati da dama kuma ta wanke su kafin daga bisani ta rufe asusun gwamnatin.
Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Osun, Oluwole Jimi-Bada (SAN), ya ce gwamnan ya ba shi umarnin shigar da kara kan EFCC bayan hukumar ta rufe asusun gwamnatin jihar.

Source: Original
Gwamna Adeleke ya ja kunnen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar an gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin adalci da gaskiya.
Adeleke ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin yin maguɗin zaɓen ranar 15 ga Agusta na iya jawo rikicin siyasa irin wanda ya faru a shekarar 1983.
Asali: Legit.ng


