Gwamnatin Katsina Ta Yi Magana kan Sace Janar da Matarsa, Ta Fadi Kokarin da Take Yi

Gwamnatin Katsina Ta Yi Magana kan Sace Janar da Matarsa, Ta Fadi Kokarin da Take Yi

  • Gwamnatin jihar Katsina ta yi karin bayani kan sace tsohon janar tare da matarsa da 'yan bindiga suka yi
  • Ta bayyana cewa an tsara sace Janar din ne da matarsa bayan da aka biyo sawunsu tun daga Kaduna inda suka fara tafiyarsu
  • Gwamnatin ta bayyana cewa tana bakin kokarinta domin ganin an kubutar da su tare da sauran mutanen da ke tsare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta tsananta ayyukanta na tsaro ta fannoni daban-daban domin ganin an ceto tsohon daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), matarsa, da sauran mutanen da ke tsare a hannun 'yan bindiga.

Gwamnatin Katsina ta nuna kyakkyawan zato cewa ƙoƙarin da ake yi zai ba da sakamako mai kyau nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Alkawarin da aka yi wa tsohon minista bayan sace yayarsa da ƴaƴanta 2

Gwamnatin Katsina na kokarin ceto Manjo Janar Rabe Abubakar
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa hakam na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar Katsina, Dr. Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Asabar, 6 ga watan Yunin 2026.

Wane kokari gwamnatin Katsina ke yi?

Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Dikko Radda ya ba da umarni ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su ba da fifiko ga ceto Rabe Abubakar, matarsa, da sauran mutanen da aka sace cikin koshin lafiya.

A cewar gwamnatin, binciken farko ya bayyana cewa satar ba fadowa kawai ta yi ba, a'a, shiri ne na musamman da ƙungiyoyin masu laifi suka tsara shi da gangan, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Shaidun da hukumomin tsaro suka tattara sun nuna cewa an sanya ido tare da bin sawun tsohon janar ɗin da matarsa tun daga Kaduna, inda suka fara tafiyarsu, kafin aka tare su kuma aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Babban basarake a Kebbi ya samo mafita ga mutanensa kan matsalar 'yan bindiga

'Yan bindiga na amfani da dabaru

Gwamnatin Katsina ta lura cewa sarkakiya da ke tattare da wannan aiki tana nuna wani sauyi mai tada hankali a cikin dabarun da ƙungiyoyin masu laifi ke amfani da su a cikin yankin.

“Gwamnati tana aiki ba dare ba rana, tana amfani da fasaha da kuma bayanan sirri na ƙasa domin matsawa masu garkuwar lamba. Babban burinmu shi ne dawo da Janar ɗin, matarsa, da sauran mutane da ke cikin makamancin wannan yanayi lafiya.”

- Dr. Bala Salisu Zango

Gwamnatin jihar Katsina ta siffanta harin a matsayin cin mutunci ba wai kawai ga tsohon jami'in sojan da iyalansa ba, har ma ga dukkan 'yan ƙasa da suka sadaukar da rayuwarsu ga hidimar ƙasa.

Sai dai, ta sake jaddada ƙudurinta na ganin an gurfanar da waɗanda ke da alhakin satar gaban shari'a tare da tarwatsa cibiyoyin masu laifi da ke bayan irin waɗannan hare-hare.

Gwamnatin Katsina na kokarin ceto Rabe Abubakar
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnatin Katsina ta hada kai da rundunar sojoji

Kara karanta wannan

Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe

A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ceto da ake gudanarwa, jihar ta ƙarfafa haɗin gwiwa da rundunar sojan kasa ta Najeriya, 'yan Sanda, da sauran hukumomin binciken sirri da na tsaro yayin da take ci gaba da sanya ido da kuma kasancewar dakarun tsaro a yankin da abin ya shafa.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama'a da su samar da bayanai game da duk wani zirga-zirga ko ayyuka na zargi da ka iya faruwa kafin aukuwar lamarin, inda ta jaddada cewa irin waɗannan bayanan sirri za su iya kasancewa masu matakar muhimmanci wajen bankado cibiyar masu laifin da ke da alhakin yin garkuwa da mutanen.

'Yan bindiga sun saki bidiyon Janar

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun saki wani bidiyon tsohon Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya da matarsa da suka yi garkuwa da su.

Matar tsohon sojan, Hajiya Amina Abubakar da mijinta sun roki gwamnati da ta kawo musu dauki bayan sace su.

Hajiya Amina Abubakar ta bayyana cewa masu garkuwar suna neman a sako wasu mutane uku masu suna Sani, Aminu da Nasiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng