Abubuwan Sani game da Manjo Janar Rabe Abubakar da Ya Mutu a hannun 'Yan bindiga
Jihar Katsina - Tsohon mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga a jihar Katsina.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Manjo Janar Rabe Abubakar ya rasu ne a hannun 'yan bindiga a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026, bayan ya yi wasu kwanaki tsare a hannunsu.

Source: Twitter
An sanar da rasuwar Manjo Janar Rabe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Nasir Muazu, ya fitar a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026, wadda Maiwada Danmallam ya sanya a Facebook.
Yadda 'yan bindiga suka sace Janar Rabe
A ranar Asabar, 30 ga watan Mayun 2026 ne dai 'yan bindiga suka sace Janar Rabe da matarsa a Katsina, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.
'Yan bindigan sun yi awon gaba da su ne da tsakar rana a yankin Matazu, lokacin da suke kan hanyar zuwa Katsina domin halartar wani bikin aure.
An dai tare hanyar da tsohon sojan suke bi tare da bude wa motar wuta kafin 'yan bindigan su yi awon gaba da shi da matarsa zuwa cikin daji.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa direban tsohon Janar din ya samu damar tserewa duk da cewa ya samu raunin harbi a lokacin harin.
Bukatun da 'yan bindiga suka nema
Bayan sace Manjo Janar Rabe, 'yan bindiga sun mika bukatunsu ga gwamnati, wadanda suke so a cika kafin su sake shi tare da matarsa.
A cikin wani faifan bidiyo da Bakatsine ya sanya a shafinsa na X da aka yi wa mutanen biyu, sun bayyana cewa 'yan bindigan na neman a sako wasu mutanensu da ke tsare a hannun hukumomi.
Matar Janar din ta bayyana cewa masu garkuwar suna neman a sako wasu mutane uku masu suna Sani, Aminu da Nasiru.
Ta ce masu garkuwar sun kuma bukaci a mayar musu da wasu dabbobi da suke zargin jami'an tsaro sun kwace.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi
Manjo Janar Rabe ya rasu hannun 'yan bindiga
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun 'yan bindiga.
A cewar sanarwar da Gwamnatin Katsina ta fitar, tsohon janar din ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon sukari da kuma hawan jini.
Gwamnatin Katsina ta bayyana rasuwar Janar Rabe a matsayin babban abin takaici ga iyalansa da kasa baki daya, inda ta bayyana cewa kokarin kubutar da shi da aka yi, bai samu nasara ba.
Wane ne Manjo Janar Rabe Abubakar?
Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar dan asalin karamar hukumar Batsari ne ta jihar Katsina, inda aka haife shi a ranar, 7 ga watan Afrilun 1965, rahoton BBC Hausa ya tabbatar da hakan.
Manjo Janar Rabe Abubakar ya yi karatun firamare da sakandare, daga baya ya yi digiri a fannin tarihi, kafin daga karshe ya shiga aikin soja.
Marigayin ya fara aikin soja ne a shekarar 1989, inda ya fito da muƙamin laftanal, sannan daga nan ya yi aikace-aikace da dama a wurare daban-daban.

Kara karanta wannan
Bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar, an ji halin da matarsa ke ciki a hannun 'yan bindiga

Source: Twitter
Mukaman da Manjo Janar Rabe ya rike
Daga cikin muƙaman da ya riƙe akwai shugaban sashen watsa labarai na hedkwatar aikin soji na musamman a yankin Neja Delta.
Ya kuma rike kwamandan makarantar horar da jami'an hulɗa da jama'a na rundunar sojojin kasa ta Najeriya wato NASPRI da ke jihar Legas.
Marigayin ya kuma taba rike mukamin babban daraktan hulɗa da jama'a a kamfanin jin daɗi da walwalar sojojin kasa na Najeriya.
Manjo Janar Rabe Abubakar ya je kasashen waje domin samun horo, inda daga cikinsu akwai kasar China.
Marigayin ya samu mukamin mai magana da yawun hedkwatar tsaron Najeriya, a watan Agustan shekarar 2015.
DHQ ta yi jajen rasuwar Manjo Janar Rabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan rasuwar da Manjo Janar Abubakar Rabe, ya yi a hannun 'yan bindiga.
Hedkwatar tsaro ta kasa bayyana jimaminta kan rasuwar tsohon daraktan yaɗa labaran na ta a cikn wata sanarwa da ta fitar.
Ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokan aikinsa da daukacin ’yan Najeriya , inda ta bayyana cewa marigayin ya yi wa ƙasa hidima cikin kwarewa da sadaukarwa,
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
