Yan Bindiga Sun Kutsa Fadar Sarki da Dare, Sun Bindige Matarsa bayan Garkuwa da Shi
- Wasu 'yan bindiga sun kutsa wani kauyen tare da sace basaraken garin yayin wani mummunan hari da suka kai
- Matar basaraken ta samu raunin harbin bindiga a hannunta yayin harin, kuma tana samun kulawa ta magani a asibiti
- Rundunar 'yan sanda ta fara aikin ceto tare da baza jami'an tsaro domin kubutar da wanda aka sace da kamo masu laifin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ode Oriya, Ondo - Wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Ode Oriya da ke karamar hukumar Owo a Ondo, inda suka yi garkuwa da sarkin yankin, Adeniyi Adelana.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun shiga garin ne da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Asabar 13 ga watan Yunin 2026.

Source: Original
Ƴan bindiga sun tsere da sarki cikin daji
An ce maharan sun nufi gidan basaraken mai shekaru 60, inda suka tilasta fitar da shi tare da tafiya da shi ta wata hanyar daji zuwa wani wuri da ba a sani ba, cewar Punch.
Lamarin ya jefa mazauna yankin cikin fargaba da tashin hankali wanda ba su taɓa shiga irinsa ba nan kusa.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Ondo, DSP Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar lamarin a tattaunawa da ƴan jarida.
Ya ce rahotannin farko sun nuna cewa ƴan bindiga shida dauke da makamai ne suka kutsa gidan Adeniyi Adelana, Baalen kauyen Ode Oriya.
Jimoh ya ce bayan samun rahoton gaggawa, jami'in 'yan sanda mai kula da B Division da ke Owo ya tattara jami'ai tare da sauran hukumomin tsaro domin isa wurin cikin gaggawa.
Ya bayyana cewa yan bindiga sun harbi matar sarkin wacce ta samu raunin harbin bindiga a hannunta na dama yayin harin.
An yi nasarar ceto ta tare da kai ta wani asibiti da ke kusa domin samun kulawar likitoci.

Source: Twitter
Halin da matar sarkin ke ciki
A cewarsa, matar na amsar magani kuma tana samun sauki yadda ya kamata, yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da aikin ceto.
Ya kara da cewa an kara tura jami'an tsaro a yankin da kauyukan da ke makwabtaka domin karfafa ayyukan tsaro.
Hakan zai taimaka wajen gano inda maharan suka nufa da kuma dakile duk wata barazana.
Jimoh ya ce Kwamishinan 'yan sandan Ondo, Felix Ohagwu, ya umurci dukkan sassan yaki da laifuffuka, jami'an tattara bayanan sirri da tawagogin aiki su kara zage damtse domin ceto wanda aka sace, Sahara Reporters ta tabbatar.
Ya jaddada cewa rundunar 'yan sanda za ta ci gaba da kokarin ganin an kubutar da Adeniyi Adelana cikin koshin lafiya tare da tabbatar da cewa duk wadanda suke da hannu a harin sun fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
Sarki ya riga mu gidan gaskiya a Ekiti
A baya, an ji cewa Gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi alhinin rasuwar babban basarake wanda ya ba da gudummawa mai yawa.
Marigayin wanda shi ne Alawe na Ilawe Ekiti, Oba Adebanji Alabi ya yi bankwana da duniya ne bayan fama da rashin lafiya.
Oyebanji ya bayyana marigayin a matsayin ma’ajiyar tarihi, ilimi da al’adu, wanda mulkinsa ya kawo zaman lafiya da ci gaba a Ilawe Ekiti.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

