Yadda Aka Birne Janar Rabe da Ya Rasu a hannun ’Yan Bindiga cikin Jimami a Katsina
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da jana’izar Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) a Katsina bisa tsarin addinin Musulunci
- An sace shi tare da matarsa a hanyar Marabar Musawa–Kafinsoli, daga baya ya rasu bayan makonni biyu yana hannun masu garkuwa da mutane
- Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana marigayi a matsayin jarumi mai kishin kasa, tare da tabbatar da ci gaba da bincike da kama masu laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - An birne Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya), wanda ya rasu makonni biyu bayan sace shi da ‘yan bindiga a Katsina.
An sace shi tare da matarsa a ranar 30 ga Mayu 2026 a kan hanyar Marabar Musawa–Kafinsoli a Jihar Katsina a lokacin harin ‘yan bindiga.

Source: Facebook
Rahoton Channels TV ya tabbatar da cewa an gudanar da jana'izar marigayin bisa koyarwar addinin Musulunci inda mutane da dama suka halarta.

Kara karanta wannan
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi maganar mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan Bindiga
Yadda Rabe Abubakar ya mutu hannun ƴan bindiga
Rahotanni sun ce ya rasu bayan makonni biyu yana hannun masu garkuwa da mutane kafin a tabbatar da mutuwarsa cikin tsananin rashin lafiya.
An gudanar da jana’izar a garin Katsina cikin tsari na addinin Musulunci, inda aka rika karatun Alƙur’ani da kuka daga jama’a da iyalai kwarai, cewar Daily Post.
Masu jimami sun yi ta kuka, inda da dama suka bayyana mutuwarsa a matsayin wata abin takaici musamman ga mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare Najeriya.
Mazauna birnin Katsina sun nuna mamaki da bakin ciki kan lamarin, suna koka cewa rashin tsaro na ci gaba da ɗaukar rayukan fararen hula da kuma waɗanda suka taɓa yin hidima a cikin soja.

Source: Original
Mazaunin Katsina ya yi alhinin rashin marigayin
Wani mazaunin Katsina, Sama’ila Balarabe, ya ce lamarin abin takaici ne wanda ya taba al'umma baki daya, ya ce:
"Wannan mummunan rashi ne ba ga iyali kawai har ma da sauran al'ummar Najeriya baki daya

Kara karanta wannan
Bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar, an ji halin da matarsa ke ciki a hannun 'yan bindiga
Hedikwatar Tsaron Najeriya ta bayyana marigayi a matsayin jami’in da ya yi hidima wajen yaki da ta’addanci a kasar tare da alkawarin bin doka.
Ga da dama daga cikin masu jimami a wurin jana’izar, mutuwar marigayi janar ta girgiza mutane wanda ke nuna ainihi mai radadi da dubban ’yan Najeriya ke fuskanta.
A cewarsu, rasuwarsa ta kara zafafa kiraye-kirayen daukar matakan gaggawa da tsauri domin magance fashi, sace-sacen mutane da sauran laifuffukan tashin hankali da ke ci gaba da barazana ga rayuka da hanyoyin samun abin dogaro a arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na rike da matar Janar Rabe
Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa har yanzu Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tana hannun ’yan bindiga.
An sace ma’auratan ne a jihar Katsina bayan an kai musu hari a kan hanyarsu ta zuwa wurin biki, lamarin da ya yi ajalin tsohon sojan.
Gwamnatin Katsina ta tabbatar da mutuwar Janar Rabe yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto matarsa da ke tsare a daji na tsawon kwanaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng