Da Gaske an Yi Sauye Sauye game da Zaben 2027? INEC Ta Magantu
- Hukumar INEC ta bayyana cewa ba ta fitar da wani sabon jadawalin kamfen na zaben 2027 kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta ba
- Hukumar ta ce jadawalin da ke yawo na bogi ne, tana mai jaddada cewa duk bayanan kamfen suna cikin jadawalin hukuma da ta fitar tun Fabrairun 2026
- INEC ta bukaci kafafen yada labarai da al'umma su rika tabbatar da bayanan zabe ta hanyoyin sadarwar hukuma domin gujewa yada labaran karya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta sauya jadawalin yakin neman zaben shekarar 2027.
Rahoto ya nuna cewa hukumar ta bayyana cewa hoton jadawalin da ake yadawa a intanet na bogi ne, kuma ba daga INEC ya fito ba.

Kara karanta wannan
'Ba Abuja ba ne,' 'Yan sanda sun gano jihar da 'yan ta'adda suka kashe babban soja

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Adedayo Oketola, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan rahoton da ya bazu.
INEC ta yi karin haske
Oketola ya ce hukumar ba ta saba fitar da jadawalin kamfen daban ba, domin dukkan bayanan da suka shafi yakin neman zabe suna cikin jadawalin ayyukan zaben 2027 da aka sake fasalinsa.
The Cable ta rahoto ya ce:
"Wannan jadawali da ake yadawa bai fito daga INEC ba. Hukumar ba ta fitar da jadawalin kamfen daban."
"Dukkan jadawalin yakin neman zabe yana cikin jadawalin ayyukan zaben 2027 da aka fitar a ranar 26 ga Fabrairu, 2026."
Ya bukaci kafafen yada labarai da sauran al'umma su tabbatar da duk wani bayani da ya shafi zabe ta hanyoyin sadarwar hukuma na INEC.
Jadawalin zaben 2027
INEC ta bayyana cewa zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya zai gudana ne a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno
Haka kuma, za a gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
A karkashin jadawalin hukuma, yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya zai fara ne a ranar 19 ga Agusta, 2026, sannan ya kare a ranar 14 ga Janairu, 2027.

Source: Facebook
Yayin da yakin neman zaben gwamnoni da na majalisun jihohi zai fara a ranar 9 ga Satumba, 2026, kuma ya kare a ranar 4 ga Fabrairu, 2027, sa'o'i 24 kafin gudanar da zaben.
Hakan ya nuna cewa babu wani sauyi da aka samu a kan lokacin kafa kamfen, kuma komai zai tafi kamar yadda aka tsara.
Abdulsalami ya ba INEC shawara
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya bukaci INEC ta kasance mai adalci ga dukkan jam'iyyun siyasa.
Ya bayyana hakan ne lokacin da shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da sauran kwamishinonin hukumar suka kai masa ziyara a gidansa da ke Minna a jihar Neja.
Janar Abdulsalami ya ce ya zama wajibi hukumar ta gudanar da zabukan 2027 cikin gaskiya, adalci da sahihanci domin kara karfafa dimokuradiyyar Najeriya.
Asali: Legit.ng