
Labaran garkuwa da mutane







Wasu miyagun ƴan bindiga sun shiga garuruwa biyu a yankin ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna, sun kashe mutane 2 sun yi awon gaba da wasu biyar ranar Litinin.

Wasu mahara da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi ajalin dan acaɓa, sun sace mai martaba sarki a jihar Edo, ƴan sanda sun bazama aikin ceto.

Sojojin Najeriya sun kai farmaki maboyar 'yan bindiga a jihar Taraba sun kama miyagu 23. 'Yan ta'addar sun biya wani basarake N1.5m domin kafa sansani.

An yi zama a kotu kan tuhumar mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, inda ya bukaci sassauci kan zargin da ake yi masa.

Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Abia, Farfesa George Chima a gidansa da ke jihar Imo,

'Yan bindiga dauke da bindigogi sun kai hari birnin tarayya Abuja cikin dare. Sun sace mata da miji da dansu da wani bako da suka yi, sun hada da wani mutum a gona.

Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa an samu nasarar cafke daya daga cikin mutanen da su ka kai hari tare da garkuwa da mutane a jihar.

Gwamnatin jihar Anambra ta rusa wani hotel da aka mayar da shi maboyar masu garkuwa da mutane. Ana zargin suna birne mutane, an samu kaburbura 30.

Kwanaki kadan bayan gwamnan Anambra ya kaddamar da rundunar tsaro dole. yan bindiga da sun takale shi da suka sace kwararreɓ likitan NAUTH a Nnewi.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari