'Yan Ta'adda Sun Shiga Kaduna da Dare, Sun Kashe Rayuka 30 Sun Kona Gidaje

'Yan Ta'adda Sun Shiga Kaduna da Dare, Sun Kashe Rayuka 30 Sun Kona Gidaje

  • Akalla mutum 30, ciki har da yara takwas, sun rasa rayukansu bayan wasu 'yan ta'adda sun kai hari ƙauyen Naridon da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna
  • Maharan sun yi harbe-harbe ba tare da nuna bambanci ba tare da ƙona gidaje da shaguna, lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin jimami
  • Gwamnatin Kaduna da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar sun yi Allah wadai da harin, yayin da mazauna suka koka kan jinkirin isowar jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kaduna – Akalla mutum 30, ciki har da yara takwas, sun mutu bayan wasu 'yan ta'adda sun kai mummunan hari ƙauyen Naridon da ke gundumar Kamaru a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare ranar Lahadi, inda maharan suka riƙa harbin mutane ba tare da nuna bambanci ba tare da banka wa gidaje da shaguna wuta.

Kara karanta wannan

Dakaru sun bazama farautar Dogo Gide da fitanannun yan bindiga 3 a Zamfara

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Punch ta rahoto cewa sakataren shugaban ƙauyen Naridon, Dogon Rana, ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa mutane huɗu da suka jikkata na ci gaba da karɓar magani, kuma ana fargabar adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa.

Halin da harin ya jefa al'umma

Dogon Rana ya bayyana cewa harin ya yi wa al'ummar ƙauyen mummunar illa, inda iyalai da dama suka rasa 'yan uwansu tare da asarar dukiyoyin da suka kai miliyoyin Naira.

Ya ce akwai wani mutum da ya rasa 'ya'yansa biyar a cikin dare ɗaya, yayin da yaro guda ɗaya da ya tsira ke kwance cikin mawuyacin hali yana karɓar magani.

Reuters ta rahoto cewa wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yi zargin cewa mutum 22 daga gida ɗaya sun mutu a harin, yayin da aka lalata shaguna da sauran kadarori.

Batun rashin isowar jami'an tsaro

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban dan siyasa, matarsa da 'ya'yansa a Zamfara

Mazauna yankin sun yi zargin cewa harin ya ɗauki kusan sa'o'i uku ba tare da jami'an tsaro sun kai ɗauki ba, duk da kasancewar sansanonin tsaro a yankunan da ke kusa.

Dogon Rana ya kuma danganta babbar matsalar da aka samu da rashin kyakkyawar hanyar mota zuwa ƙauyen, yana mai cewa hakan ya hana jami'an agaji isa cikin lokaci tare da rage damar jama'a na tserewa.

Gwamna Uba Sani
Uba Sani a wajen taron siyasa a Kaduna. Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Harin ya jawo Allah wadai daga gwamnatin jihar Kaduna, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar PDP, Usman Bawa.

An kai hari wajen raba katin zaɓe

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari wata cibiyar tattara sakamakon zaɓe da ake raba katin zaɓe na dindindin (PVC) a yankin Okuku da ke jihar Osun.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga harabar cibiyar tare da yin harbi sama kafin su kwashe wasu kayayyaki da suka haɗa da katunan PVC, lamarin da ya haddasa firgici da tarwatsa aikin.

Shaidun gani da ido sun ce jami'an hukumar INEC da mutanen da suka je karɓar katunansu sun tsere domin tsira da rayukansu yayin da aka dakatar da aikin na ɗan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng