Yan Bindiga Sun Fitar da Sabon Bidiyo, Tsohon Janar, Matarsa Sun Roki Gwamnati
- Miyagun yan bindiga sun fitar da sabon bidiyon tsohon Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya da matarsa da aka sace
- Masu garkuwar sun bukaci a sako wasu mutane uku da suke tsare tare da mayar musu da dabbobin da suka ce an kwace
- Janar din mai ritaya ya yi kira ga zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha'awar tattaunawa da zaman tare cikin lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Yan bindiga sun saki wani bidiyon tsohon Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya da matarsa da suka sace.
Matar tsohon sojan, Hajiya Amina Abubakar da mijinta sun roki gwamnati da ta kawo musu dauki bayan sace su.

Source: Twitter
Masu garkuwar sun saki wani bidiyon wanda Daily Trust ta bibiya da ya nuna ma'auratan a hannunsu, yayin da suke bayyana bukatun wadanda suka yi garkuwar.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Abubuwa 4 da 'yan ta'adda suka nema kafin su sako dalibai da malaman Oyo
Abin da yan bindiga ke bukata
A cikin bidiyon mai tsawon mintuna hudu da dakika biyu, an ga ma'auratan tsaye suna isar da sakonnin masu garkuwar.
Matar Janar din ta bayyana cewa masu garkuwar suna neman a sako wasu mutane uku masu suna Sani, Aminu da Nasiru.
Ta ce masu garkuwar sun kuma bukaci a mayar musu da wasu dabbobi da suke zargin jami'an tsaro sun kwace.
Yan bindiga 3 da ke hannun gwamnatin Katsina
A cewarta, an kama mutum biyu daga cikin wadanda ake nema a Jikamshi, yayin da aka kama na ukun a Kano.
Ta roki gwamnatin Katsina da shugabannin kananan hukumomi biyar da su taimaka wajen cika wadannan bukatu domin samun 'yancinsu.

Source: Original
Abin da tsohon Janar din ya ce
Shi ma Janar Rabe mai ritaya ya yi magana kadan a bidiyon, inda ya bukaci a yi kokarin samar da zaman lafiya.
Ya ce masu garkuwar sun nuna sha'awar yin tattaunawa da neman hanyar zama tare cikin lumana da al'ummomi.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi dabara sun cafke 'dan bindiga Kachalla Halilu da ya shiga kasuwa tsakar rana
A duk tsawon bidiyon, babu inda masu garkuwar suka ambaci bukatar a biya kudin fansa domin sakin wadanda suka sace.
Wane martanin gwamnatin Katsina ta yi?
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gwamnatin Katsina da jami'an tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan bidiyon ba, cewar Punch.
Mutane da dama sun nuna damuwa game karuwar hare-hare a yankunan karkara musamman na Arewacin Najeriya.
Jihar Katsina na daga cikin jihohi da ke fama da farmakin yan ta'adda wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin al'ummar yankuna da dama.
Bukatar yan bindiga bayan sace tsohon Janar
A wani labarin cewa an samu labarin cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya).
Jagoran 'yan bindigan da suka yi garkuwa da tsohon Janar din tare da matarsa ya tuntubi iyalansa bayan sace shi inda ya bayyana cewa ita ce hanya daya kacal na kubutar da su.
Majiyoyi sun bayyana cewa Kachallah Muhammad ya mika bukatarsa ga gwamnati ta hannun iyalan tsohon kakakin sojojin.
Asali: Legit.ng