Yadda Aka Karbo Gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan Ya Rasu a hannun 'Yan Bindiga

Yadda Aka Karbo Gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan Ya Rasu a hannun 'Yan Bindiga

  • Sababbin bayanai masu karo da juna sun fito kan yadda aka karbo gawar Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) daga wurin 'yan bindiga
  • Iyalan tsohon kakakin rundunar soji sun musanta ikirarin cewa Janar Rabe ya rasu sakamakon ciwon sukari da hawan jini
  • Babu wata sanarwa a hukumance daga hukumar sojoji ko gwamnatin jihar Katsina kan yadda aka dauko gawar marigayin daga daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Sababbin bayanai masu cin karo da juna sun kara jefa rudani kan yadda aka karbo gawar Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) daga wurin yan bindiga.

Wannan na zuwa ne yayin da iyalansa suka nuna shakku kan bayanin da gwamnati ta bayar game da musabbabin mutuwarsa a hannun masu garkuwa da mutane.

Rabe.
Marigayi tsohon kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Premium Times ta tunatar da cewa an sace Rabe tare da matarsa, Hajiya Amina, a ranar 30 ga Mayu, 2026, a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke karamar hukumar Matazu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Khan Salihu ya rasu bayan ya dawo daga masallaci

Daga baya Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwarsa, inda ta ce ya mutu ne sakamakon matsalolin da suka shafi ciwon sukari da hawan jini.

Sai dai ’yan uwansa sun yi watsi da wannan bayani, suna masu cewa marigayin bai taba fama da wadannan cututtuka ba.

Yadda aka an karbo gawar Janar Rabe

Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa masu garkuwa ne suka ba jami’an gwamnati umarnin zuwa wani wuri kusa da garin Karaduwa domin karbar gawar marigayin.

Majiyar ta shaida wa Premium Times cewa an tura motar daukar marasa lafiya zuwa yankin bayan an samu sako daga masu garkuwa da mutanen.

A cewarta, an gargadi wadanda suka je wurin da kada su zo tare da jami’an tsaro.

“Sun ce ba sa son ganin jami’an tsaro a wurin,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa bayan motar daukar marasa lafiyan ta isa kusa da gadar Karaduwa, an umurci direban ya juya motar zuwa bangaren Matazu daga bisani 'yan bindigar suka iso kan babura dauke da gawar.

Kara karanta wannan

Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito

Bayan mika gawar, an ce sun gargadi wadanda ke wurin da kada su taba gawar har sai sun bar yankin. Daga nan ne aka kai gawar zuwa Matazu kafin sojoji su yi wa motar rakiyar tsaro zuwa Katsina.

Katsina map.
Taswirar jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma Hoto: Legit.ng
Source: Original

An samu wani bayani na daban

Sai dai wata majiya daga yankin ta bayar da wani labari na daban. A cewarta, wasu mazauna yankin ne suka gano gawar a kusa da wani wurin yankan katako a Karaduwa.

“Mutane ne suka gano gawar sannan suka sanar da jami’an tsaro, wadanda suka zo suka tabbatar da ko wanene sannan suka dauke ta cikin motar asibiti zuwa Katsina tare da rakiyar sojoji,” in ji majiyar.

Har zuwa yanzu babu wata hanyar da aka tabbatar da daya daga cikin wadannan bayanai, kuma hukumomin soji ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan yadda aka samu gawar ba.

Sojoji sun ceto matar Janar Rabe

A baya, kun ji cewa dakarun Operation Fansan Yanma sun ceto matar marigayi Janar Rabe Abubakar bayan wani farmaki da suka kai jihar Katsina.

Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne karkashin sabon samamen Operation Clean Sweep III a karamar hukumar Matazu.

Hukumomin soji sun bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da samame a yankin domin cafke ‘yan bindigar da suka tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262