Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Manjo Janar da Matarsa a Katsina
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya da matarsa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani biki a Katsina
- Maharan sun bude wa motar da suke ciki wuta, inda direbansa ya tsira da raunin harbi yayin da aka tafi da ma’auratan cikin daji
- Harin ya zo ne kwanaki kadan bayan 'yan bindiga sun kashe mutane 16 a kauyen Kiliya da ke karamar hukumar Dutsinma ta Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Katsina - Tsohon Daraktan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, da matarsa sun fada hannun ‘yan bindiga a jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Matazu yayin da tsohon hafsan sojan ke tafiya zuwa jihar Katsina domin halartar wani bikin aure.

Source: Original
'Yan bindiga sun sace tsohon Janar a soja
Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa maharan sun tare hanyar da tsohon sojan suke bi tare da bude wa motar wuta kafin su yi awon gaba da shi da matarsa zuwa cikin daji, in ji rahoton Daily Trust.
An ce direban tsohon Janar din ya samu damar tserewa duk da cewa ya samu raunin harbi a lokacin harin.
A wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an ga motar kirar Peugeot 406 mai launin ja da ma’auratan ke ciki a harabar Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Matazu.
Wakilan kafafen yada labarai sun lura da akalla ramukan harsashi guda biyu a jikin motar, lamarin da ke nuna yadda aka kai harin.
Hari na biyu kan tsohon Janar a Katsina
Wannan shi ne karo na biyu da aka samu wani mummunan hari da ya shafi tsohon babban jami’in soja a jihar Katsina cikin dan kankanin lokaci.
A shekarar 2025, ‘yan bindiga sun sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya, tsohon Darakta Janar na Hukumar Yi wa Kasa Hidima ta Kasa (NYSC).
Tsiga ya shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa kafin daga bisani ya samu ‘yanci, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Source: Twitter
Katsina na ci gaba da fama da matsalar tsaro
Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga duk da kokarin da hukumomi ke yi na dawo da zaman lafiya.
Lamarin sace tsohon Janar din ya zo ne bayan wani mummunan hari da aka kai kauyen Kiliya da ke karamar hukumar Dutsinma a ranar Juma’a, in ji rahoton Punch.
Maharan sun kai harin ne bayan an kammala sallar Juma’a yayin da al’umma ke cikin shagulgulan Babbar Sallah.
Wani mazaunin kauyen ya ce mutane suna zaune suna hira bayan sallah lokacin da ‘yan bindiga suka afka musu.

Kara karanta wannan
Mai dokar barci: Sojoji sun damke 'dan bijilanti da zargin yi wa ISWAP leken asiri
Ya ce maharan sun umarci mutane su tsaya kafin daga bisani su fara harbe-harbe kan mazauna yankin da masu wucewa.
Yadda aka sace Janar Tsiga a Katsina
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun shiga garin Tsiga, ƙaramar hukumar Bakori a Katsina, sun yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na NYSC, Maharazu Tsiga.
An tattaro cewa ƴan ta'addar sun afka garin ne da tsakar dare misalin ƙarfe 12:30, sun ɗauki mutane da dama har da Janar Tsiga mai ritaya.
'Dan majalisar Bakori da Ɗanja, Hon. Abdullahi Balarabe Dabai ya tabbatar da lamarin, ya miƙa jaje ga al'ummar yankin da Katsina baki ɗaya.
Asali: Legit.ng

