Juyin Mulki: An Gano Yadda Malaman Addini Suka Karbi Miliyoyi Amma da Wani Nufi

Juyin Mulki: An Gano Yadda Malaman Addini Suka Karbi Miliyoyi Amma da Wani Nufi

  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa malaman Musulunci sun karbi miliyoyi a yunkurin juyin mulkin da aka yi a Najeriya
  • Malaman addinin Musulunci da aka ambata sun shaida wa masu bincike cewa sun yi kokarin hana shi ci gaba da aikata wannan laifi
  • Daya daga cikin malaman ya ce ya karbi miliyoyin Naira domin addu'a da ayyukan alheri, yana musanta cewa ya goyi bayan yunkurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Binciken musamman na ya yi gano wasu bayanai kan Kanal Mohammed Ma’aji na rundunar sojin Najeriya, wanda ake zargi da jagorantar yunkurin juyin mulkin 2025.

An ce Ma'aji ya nemi goyon bayan malamai domin samun nasarar shirinsa. Rahoton ya ce baya ga makamai da hadin kan sojoji, ya kuma nemi taimakon addu'o'i.

Yadda malaman Musulunci suka karbi miliyoyi a shirin juyin mulki
Wanda ake zargi da kitsa juyin mulki, Kanal Ma'aji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Takardun bincike da jaridar Premium Times ta samu sun nuna cewa Ma’aji ya rika tuntuɓar malaman Musulunci domin neman addu'a, shiriya da goyon bayan ruhaniya.

Kara karanta wannan

'Babu yan bindiga a Niger': Gwamnati ta gano yadda aka samu rashin tsaro

Abin da malamai suka yi yunkurin yi

Rahoton ya ce malaman da aka yi magana da su sun bayyana wa masu bincike cewa ba su taba goyon bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

Maimakon haka, sun ce sun yi kokarin dakatar da abin da Ma’aji ya rika kira da shirin tayar da tarzoma.

Daya daga cikin malaman, Bukar Goni, ya ce ya fara sanin Ma’aji ne ta hannun Manjo M.A. Usman.

Ya ce Kanal din ya kasance cikin damuwa saboda ya kasa cin jarabawar karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar sau da dama.

Bukar Goni ya bayyana cewa Ma’aji ya rika turo masa kudi daga N300,000 zuwa N1 miliyan domin yin sadaka da addu'a.

Bayan ya sake faduwa jarabawar karin girma, Kanal din ya kara bayyana masa cewa wasu a cikin rundunar ba sa son ya ci gaba.

Malamin ya ce daga baya Ma’aji ya fara maganar wasu matasa da suke son tayar da abin da ya kira tarzoma.

Kara karanta wannan

Tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe babban jami'in soja a Najeriya

Ya ce nan take ya hana shi ci gaba da wannan tunani, yayin da Manjo Usman ya bukace shi da ya ci gaba da lallashinsa domin ya jinkirta shirin.

Bayanai sun sake fitowa kan yunkurin juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi tagumi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Dabarar da malamin Musulunci ya yi ga soja

A cewarsa, ya yi amfani da wata dabara ta tunani inda ya gaya wa Kanal din cewa zai yi wani mafarki a cikin kwanaki 20.

Bayan Ma’aji ya ba da labarin mafarkin, malamin ya fassara masa cewa gargadi ne daga Allah, lamarin da ya sa ya dakatar da shirin na wani lokaci.

Bukar Goni ya amsa cewa ya karbi makudan kudade daga Ma’aji, ciki har da kusan Naira miliyan 10 cikin kwanaki 15 da kuma wasu canja wurin kudi biyu na Naira miliyan 20.

Ya dage cewa an ba shi kudin ne domin addu'a da ayyukan alheri, ba domin wata manufar siyasa ba.

Juyin mulki: Martanin malami daga Zaria

Rahoton ya kuma ce wani malami daga Zaria mai suna Abdulkadir Sani ya bayyana cewa Ma’aji ya taba neman ya yi masa addu'a.

Ya ce bayan an sanar da shi game da shirin da ake zargi, ya gargadi masu hannu a ciki cewa ba zai yi nasara ba saboda wasu daga cikinsu za su tona asirin shirin.

Kara karanta wannan

An samu sababbin bayanai kan yadda aka sace shugaban karamar hukuma a Zamfara

Bayanai sun fito kan juyin mulkin Tinubu

An ji cewa wasu takardun bincike sama da shafuka 7,400 sun bayyana cikakken shirin da ake zargin wasu jami'an soja a juyin mulki.

Ana zargin masu shirin sun raba ayyuka tsakanin jami'ai, suka yi amfani da kalmomin sirri, tare da tsara komai.

Takardun sun kuma nuna an shirya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama, tattara sojoji da makamai, tare da kafa tsarin mulki na rikon kwarya bayan karbe iko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.