Likitan El Rufa'i Ya Rubuta Zungureriyar Takarda, Ya Yi Bayani kan Zargin ICPC
- Likitan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Dr. Bello Abubakar ya bayyana cewa bai san Mohammed Bala Aliyu ba, da ya yi rantsuwa da bayanin da ya fitar
- Hukumar ICPC na tuhumar likitan Nasir El-Rufa'i da rubuta takardar lafiya ta bogi da aka yi rantsuwa da ita wajen neman belin tsohon gwamnan a kotu
- Likitan ya bayyana yadda ya duba El-Rufai a lokuta daban-daban tun daga shekarar 2005 zuwa 2026, tare da kokarin wanke kansa daga zargin ICPC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – 'Kwararren likita kan cutar daji a Asibitin Kasa da ke Abuja, Dr. Bello Abubakar, ya musanta zargin cewa ya ƙirƙiri rahoton lafiya na bogi da aka yi amfani da shi wajen neman beli ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
A cikin bayanin da ya rubuta wa Hukumar ICPC, wanda ya bayar a gaban lauyansa, Rabiu Suleiman na kamfanin Mahmud SAN and Co., Dr. Abubakar ya amince cewa shi ne ya rubuta rahoton lafiyar.

Source: Facebook
A wasikar da jaridar Premium Times ta samu, likitan ya ce duk da shi ya rubuta wasikar, amma ya ce bai san mutumin da ake zargi ya yi amfani da rahoton wajen yin rantsuwar kotu ba.
Zargin ICPC kan likitan El-Rufa'i
Jaridar Punch ta wallafa cewa ICPC ta shigar da ƙara mai tuhume-tu hudu a kan likitan, tana zarginsa da fitar da rahoton lafiya na bogi domin yaudarar jami'in gwamnati da kuma tallafa wa bukatar belin El-Rufai.
A cewar takardar tuhumar, Dr. Abubakar ne ya rubuta rahoton mai taken "Medical Report and Expert Opinion for Urgent Medical Intervention" mai kwanan wata 10 ga Yunin 2026, duk da cewa ya san bayanan cikinsa ba gaskiya ba ne.
Har ila yau, ana zarginsa da hada baki da wani Aliyu Bala domin ƙirƙirar rahoton, ta yadda Mohammed Bala Aliyu zai yi ƙarin rantsuwar kotu da za ta goyi bayan neman belin El-Rufai.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani
Amma a cewar likitan:
"Ban san ko waye Mohammed Bala Aliyu ba, kuma ban taba hulɗa ko mu'amala da shi ba. Ko kaɗan," in ji shi.
Yadda likitan ya fara kula da El-Rufai
Dr. Abubakar ya bayyana cewa ya fara sanin El-Rufai ne ta hannun matarsa, inda ya ce shi ne ya karɓi haihuwar ɗansu na fari. Daga baya ne tsohon gwamnan ya zama ɗaya daga cikin mutanen da ya ke duba wa.
Ya ce El-Rufai ba rajista yake yi a cibiyarsa mai zaman kanta ta Belam Cancer Centre da ke Jabi ba, sai dai a Asibitin Kasa na Abuja, inda aka yi masa rajista tun kusan shekarar 2005.

Source: Facebook
Likitan ya ce yana aiki a asibitin tun lokacin da aka buɗe shi a watan Satumban 1999. Ya ce ya duba El-Rufai sau ƙasa da huɗu tsakanin shekarun 2017 zuwa 2025 a Asibitin Kasa.
Dr. Abubakar ya kara da cewa waɗannan ziyarce-ziyarcen ba a rubuce suke ba saboda ba su buƙaci hakan. A shekarar 2025 kuma, ya ce sun fi yin magana ta waya yayin da El-Rufai yake ƙasashen waje.
Likitan ya ce tsakanin watan Yuni da Yulin 2026 ya duba El-Rufai sau uku lokacin da yake tsare a hannun ICPC, bayan iyalansa sun nemi ya je.
Ya ce sau biyu daga cikin binciken an yi su ne a ofishin ICPC tare da ma'aikatan asibitin hukumar, kuma an rubuta shigarsa a wajen karɓar baƙi. Na uku kuma an yi shi ne a Asibitin Kasa.
Da yake bayani kan ziyarar ranar 9 ga Yuli, ya ce ya je tare da babban likitan da ke ƙarƙashinsa kamar yadda ƙa'ida ta tanada. Daga baya Daraktan Asibitin da Daraktan Ayyukan Lafiya suka shiga wajen duba marar lafiyar.
ICPC ta dauki mataki kan likitan El-Rufa'i
A wani labarin, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar da ƙara a gaban Hukumar Kula da Ayyukan Likitoci da Masu Haƙora ta Najeriya (MDCN), inda ta nemi a binciki tare da hukunta Farfesa Bello Abubakar.
Hukumar ICPC ta kai korafin ne saboda ta na so a binciki likitan bisa zargin samar da rahoton da ake zargin na bogi ne, kuma an yi amfani da shi wajen neman belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
ICPC ta bayyana a cikin takardar koken cewa likitan ya aikata abin da ya saba wa ƙa'idojin aikin likitanci. Ta buƙaci MDCN ta gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa tare da ɗaukar matakin ladabtarwa idan aka tabbatar da zargin.
Asali: Legit.ng

