Babbar Magana: Hisbah Ta Haramta Wasu Abubuwa da Suka Shafi Aure a Sokoto

Babbar Magana: Hisbah Ta Haramta Wasu Abubuwa da Suka Shafi Aure a Sokoto

  • Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta sanar da haramta wasu al'adu da ake yi a bukukuwa da shagulgulan aure
  • Daga cikin abubuwan da aka haramta akwai "Na Gani In So", kidan DJ, Wazigidi da wasu dabi'un da hukumar ta ce sun saba wa koyarwar Musulunci
  • Hukumar ta gargadi masu shirya bukukuwa da iyalai su bi umarnin, tana mai cewa za ta dauki mataki kan masu karya dokar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto – Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta sanar da haramta wasu al'adu da ake yi yayin bukukuwan aure da sauran tarukan jama'a, tana mai cewa sun saba wa koyarwar addinin Musulunci da kuma kyawawan dabi'un al'umma.

Dokar, wacce ta fara aiki nan take, ta haramta al'adar da aka fi sani da "Na Gani Ina So", wadda ke kunshe da kai wa iyayen amarya kayan kyauta irin su kwalayen lemo, ruwan roba, biskit, alewa da goro a matsayin gabatarwar neman aure.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun afka dakin kwanan dalibai mata na jami'ar ATBU, an yi barna mai girma

Hisbah ta haramta wasu abubuwa a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Sokoto, Malam Usman Abdullahi Jatau, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Sokoto a ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026.

Hakazalika hukumar ta haramta amfani da kidan DJ da Wazigidi a wuraren bukukuwa.

Sauran abubuwan da Hisbah ta haramta

Hukumar ta kuma haramta daura manyan lasifikoki ko amfani da kayan sauti masu karfi a kan baburan adaidaita sahu (Keke Napep), zaman mata a gefen direban adaidaita sahu, tarukan nishadi da maza da mata ke haduwa ba tare da tsari ba.

Salon aski da ta bayyana a matsayin marasa tarbiyya ga yara da matasa, da kuma kashe kudade fiye da kima wajen kayan lefe.

A cewar hukumar, wadannan dabi'u sun saba wa Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW).

Hisbah ta bayyana dalilin daukar matakin

Kwamandan na Hisbah ya bayyana cewa ce an dauki matakan ne domin inganta tarbiyya da kuma kare addini da al'adun jihar.

Kara karanta wannan

Yan sandan MOPOL sun nemi agajin Sufeton Ƴan sanda watanni 7 da hana su alawus

"Muna bayyana cewa wadannan bidi'o'i da suka saba wa Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW) suna da mummunan tasiri ga duk auren da aka gudanar ta irin wannan hanya saboda ya kauce wa koyarwar Annabi." In ji shi

Jatau ya yi kira ga iyaye, masu shirin aure da iyalan ango da amarya da su ji tsoron Allah tare da guje wa abubuwan da hukumar ta haramta.

"Muna kira ga iyalan ango da amarya da kuma iyaye da su ji tsoron Allah, su daina wadannan dabi'u," in ji shi.

Hisbah ta yi barazanar daukar mataki

Kwamandan ya gargadi cewa hukumar za ta tabbatar an aiwatar da wannan umarni ba tare da sassauci ba.

"Hukumar za ta gudanar da aikinta a duk lokacin da aka samu irin wadannan abubuwan da aka haramta, musamman idan aka nemi ta shiga tsakani," in ji shi.

Ya kuma bukaci shugabannin al'umma a dukkan gundumomi da unguwanni da su taka rawar gani wajen tabbatar da kyawawan dabi'u a tsakanin jama'a.

"Muna son shugabannin al'umma a kowace unguwa da mazaba su sauke nauyin da aka dora musu na tabbatar da tarbiyyar mutanen da suke jagoranta," ya bayyana.

Kara karanta wannan

ADC ta kalubalanci Tinubu ya ziyarci Zamfara bayan mummunan hari

Hisbah a Sokoto ta hana bidi'o'i
Shugaban Hisbah na Sokoto yayin magana da manema labarai Hoto: Sokoto State Hisbah Board
Source: Facebook

Gargadin Hisbah kan auren gata

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi gargadi ga jama’a kan shirin auren gata da ake shirye-shiryen gudanarwa.

Hisbah ta gargadi jama'a da kada su biya kudi ga duk wani mutum da ya nemi karbar kudi domin saka sunayensu cikin shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shirin gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng