Abin ba Dadi: Manjo Janar Rabe Abubakar Ya Mutu a hannun 'Yan Bindiga

Abin ba Dadi: Manjo Janar Rabe Abubakar Ya Mutu a hannun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Manjo Janar na rundunar sojojin Najeriya, Rabe Abubakar (mai ritaya)
  • Ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini da yake fama da su
  • Mai girma Gwamna Dikko Radda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar Katsina da Najeriya baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigerian - Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da matarsa a jihar Katsina, ya riga mu gidan gaskiya.

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar tsohon Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga.

Rabe.
Tsohon Manjo Janar na rundunar sojin Najeriya, Rabe Abubakar Hoto: Mobile Media Crew
Source: Twitter

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Katsina, Nasiru Mu'azu ya rattaba wa hannu a ranar 13 ga Yuni, 2026, kuma Maiwada Dammallam ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Amurka mai sukar Najeriya ya jinjina wa Tinubu kan dokar ƴan sandan jihohi

Gwamnatin Katsina ta bayyana rasuwar Janar Rabe a matsayin babban abin takaici ga iyalansa da kasa baki daya.

Sanarwar ta ce duk da kokarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suka yi domin ganin an kubutar da shi cikin koshin lafiya, hakan bai samu ba.

Abin da ya haddasa mutuwar Rabe Abubakar

A cewar Gwamnatin Katsina, tsohon janar din ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon sukari da kuma hawan jini.

Sanarwar ta bayyana cewa mutuwarsa ta kasance babban rashi ba ga iyalansa kadai ba, har ma ga Jihar Katsina da Najeriya gaba daya.

Gwamna Dikko Radda ya yi ta’aziyya

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin tare da al’ummar Najeriya.

Ya bayyana lamarin a matsayin wani lokaci mai duhu, yana mai cewa hakan ya sake nuna muhimmancin hada kai da kara kaimi wajen yaki da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuffuka da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma.

Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda yana magana a taron Majalisar zartarwa Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Wane mataki Gwamnatin Katsina ta dauka?

Kara karanta wannan

2027: Takarar Kwankwaso da Obi ta sake samun karfi, dattawa sun mara masu baya

Gwamnatin Katsina ta jaddada kudirinta na ci gaba da aiki tare da Gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin tabbatar da an kamo wadanda ke da hannu a wannan lamari tare da hukunta su.

Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yakar ‘yan bindiga da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.

An yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi, tare da bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

Yadda aka sace Manjo Janar Rabe

Tun farko, kun ji cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya da matarsa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani biki a jihar Katsina.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa maharan sun tare hanyar da tsohon sojan suke bi tare da bude wa motar wuta kafin su yi awon gaba da shi.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Matazu yayin da tsohon hafsan sojan ke tafiya zuwa jihar Katsina domin halartar wani bikin aure.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262