An Sanya Sunan Sheikh Pantami a Shafin INEC, zai Fafata da APC a 2027
- Kungiyar Pantamiyya Movement ta sanar da cewa jam'iyyar PDP ta kammala tura bayanan takarar Farfesa Isa Ali Pantami zuwa shafin hukumar INEC
- Kungiyar ta ce an sanya bayanan Pantami a ranar 26 ga Yulin 2026 bayan ya zama dan takarar gwamna ba tare da hamayya ba a zaben fitar da gwani
- Pantamiyya ta bayyana cewa hakan wata muhimmiyar nasara ce ga dimokuradiyya, tana mai nuna kwarin gwiwar samun shugabanci nagari a Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gombe – Kungiyar Pantamiyya ta bayyana cewa jam'iyyar PDP ta kammala daura bayanan takarar Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami a shafin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Gombe.
A wata sanarwar manema labarai da Farfesa Suleiman Mohammed ya sanya wa hannu a madadin kungiyar Pantamiyya, an ce an kammala aikin sanya bayanan ne a ranar 26 ga Yulin 2026.

Source: Facebook
Sanarwar da Malamin ya wallafa a Facebook ta ce wannan ya biyo bayan nasarar da Pantami ya samu a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP da aka gudanar a ranar 26 ga Mayun 2026.
Pantami ya zama dan takarar PDP
Kungiyar ta bayyana cewa Pantami ya zama dan takarar gwamna ba tare da hamayya ba bayan sauran masu son takara sun kasa samun takardar cancanta daga Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na jam'iyyar.
A cewar sanarwar, an gudanar da tsarin tabbatar da takararsa ne a karkashin sa idon jami'an INEC, inda aka tabbatar da cewa an bi duk dokoki da ka'idojin da suka dace.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Ofishin Sakataren Tsare-tsare na Kasa na PDP ya tabbatar mana da cewa an kammala sanya bayanan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a shafin INEC, tare da isar da takardar tabbatar da hakan ga dan takarar da kuma jam'iyyar."
Pantamiyya ta yabawa Pantami
Kungiyar ta bayyana Pantami a matsayin fitaccen malami, tsohon Ministan Sadarwa, kuma tsohon Darakta Janar na Hukumar NITDA.
Ta ce ya yi fice wajen gudanar da ayyukan ci gaba, inda ta yi ikirarin cewa ya kara kudin shiga a bangaren tattalin arzikin zamani da sama da 593%, tare da aiwatar da fiye da ayyuka da shirye-shirye 241 a jihar Gombe.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce idan Allah Ya ba shi nasara a 2027, Pantami na da shirin amfani da gogewarsa wajen bunkasa ilimi, noma, tattalin arzikin zamani, masana'antu, tsaro da karfafa matasa domin ci gaban jihar Gombe.
Kungiyar ta kuma gode wa shugabannin PDP na jiha da na kasa bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da wannan mataki.
An nada kwamishinoni a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rantsar da sababbin kwamishinoni da sauran manyan jami'an gwamnati domin fadada majalisar zartarwar jihar.

Kara karanta wannan
Baraka a APC, tsohon minista ya fadi matsayarsa kan amincewa da zaben fitar da gwani
Sabon tsarin ya kara yawan ma'aikatun gwamnati daga 18 zuwa 23, inda aka kirkiro sababbin ma'aikatun kula da jin kai da rage talauci da kuma bunkasa kiwo.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce matakin zai kara inganta ayyukan gwamnati tare da dacewa da manufar Renewed Hope ta shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng

