Hedkwatar Tsaron Najeriya Ta Yi Maganar Mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'Yan Bindiga

Hedkwatar Tsaron Najeriya Ta Yi Maganar Mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'Yan Bindiga

  • Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana alhini da jimaminta kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya
  • Marigayin ya mutu ne a hannun masu garkuwa bayan an sace shi tare da matarsa a Katsina a yan makonnin da suka gabata
  • Babbar hedikwatar sojojin ta jaddada cewa za ta ƙara ƙaimi wajen rusa ƙungiyoyin ta’addanci da cafke masu hannu a garkuwa da mutane

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana jimaminta kan rasuwar tsohon daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin ƙasar, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya.

Manjo Janar Rabe ya mutu ne yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane, kamar yadda Gwamnatin Katsina ta tabbatar.

Olufemi Olatubosun Oluyede.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da Manjo Janar Rabe Abubakar Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan bindiga sun sace marigayi Rabe Abubakar tare da matarsa a ranar 30 ga Mayu, 2026, a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar, an ji halin da matarsa ke ciki a hannun 'yan bindiga

Hedkwatar tsaro ta yi ta'aziyyar Rabe Abubakar

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran DHQ, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar, rundunar sojin Najeriya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokan aikinsa da daukacin ’yan Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa marigayin ya yi wa ƙasa hidima cikin kwarewa da sadaukarwa, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a rundunar soji.

Muhimman ayyukan da ya yi a gidan soja

Rundunar ta ce Janar Rabe Abubakar ya taba zama kakakin rundunonin soji daban-daban kafin daga bisani ya zama Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro.

An kuma yaba masa kan rawar da ya taka wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, bunƙasa ƙwarewar jami’an soji da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ƙarfafa rundunar sojin Najeriya.

A cewar DHQ, kishin ƙasa da jajircewarsa wajen kare haɗin kan Najeriya za su ci gaba da zama abin koyi ga jami’an rundunar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Dalilin hedkwatar tsaro na yin shiru

Kara karanta wannan

Abin ba dadi: Manjo Janar Rabe Abubakar ya mutu a hannun 'yan bindiga

Sanarwar ta bayyana cewa rundunar soji ba ta yi magana a bainar jama'a kan sace Janar Rabe ba ne saboda ƙoƙarin da ake yi na ceto shi.

Ta ce an tura dukkanin kayan aiki da dabarun da ake da su domin ganin an kuɓutar da shi cikin koshin lafiya, amma abin takaici hakan bai samu ba.

DHQ ta jaddada cewa mutuwar Janar Rabe Abubakar za ta ƙara musu kaimi a ƙudurin yaƙar ta’addanci da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar.

Hedkwatar tsaro.
Babbar hedkwatar rundunar sojojin Najeriya da ke Abuja Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

Alƙawarin dawo da zaman lafiya

Rundunar ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare martabar ƙasa da rayukan al’umma.

Ta kuma yi alƙawarin cewa za ta ci gaba da bibiyar masu aikata ta’addanci har sai an tabbatar da zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan Najeriya.

Mene ne ya yi ajalin Janar Rabe?

A dazu, kun ji cewa Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Manjo Janar na rundunar sojojin Najeriya, Rabe Abubakar (mai ritaya).

Ta ce duk da kokarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suka yi domin ganin an kubutar da shi cikin koshin lafiya, hakan bai samu ba.

A cewar Gwamnatin Katsina , tsohon janar din ya rasu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon sukari da kuma hawan jini.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262