Bayan Mutuwar Janar Rabe Abubakar, An Ji Halin da Matarsa ke Ciki a hannun 'Yan Bindiga

Bayan Mutuwar Janar Rabe Abubakar, An Ji Halin da Matarsa ke Ciki a hannun 'Yan Bindiga

  • Rahotanni sun nuna cewa har yanzu Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tana hannun ’yan bindiga
  • An sace ma’auratan ne a jihar Katsina bayan an kai musu hari a kan hanyarsu ta zuwa wurin biki, lamarin da ya yi ajalin tsohon sojan
  • Gwamnatin Katsina ta tabbatar da mutuwar Janar Rabe yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto matarsa da ke tsare a daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa har yanzu Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, na tsare a hannun masu garkuwa da mutane duk da mutuwar mijinta.

An sace Janar Rabe da mai dakinsa a ranar 30 ga Mayu, 2026, bayan da ’yan bindiga suka tare motarsu a hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi maganar mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan Bindiga

Amina Abubakar.
Hajiy Amin Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar Hoto: Katsina New Post
Source: Facebook

Abubuwan da yan bindiga suka nema

Daily Trust ta ruwaito cewa kafin rasuwarsa, an ga Janar Rabe da matarsa a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda suka bayyana bukatun masu garkuwar.

A cikin bidiyon mai tsawon mintuna huɗu da daƙiƙa biyu, an ga ma’auratan tsaye suna isar da saƙon masu garkuwar ga gwamnati da al’umma.

Hajiya Amina ta bayyana cewa masu garkuwar suna neman a saki wasu yan uwansu mutum uku da suka bayyana sunayensu da Sani, Aminu da Nasiru.

Ta kuma roƙi gwamnatin jihar Katsina da shugabannin wasu ƙananan hukumomi biyar da su taimaka wajen cika waɗannan buƙatu domin a sake su

An tabbatar da mutuwar Janar Rabe

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar Katsina, Dr Nasiru Mu’azu, ya sanar a ranar Asabar cewa Janar Rabe ya rasu ne sakamakon ciwon sukari da hawan jini da yake fama da su a hannun yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Abin ba dadi: Manjo Janar Rabe Abubakar ya mutu a hannun 'yan bindiga

Ya bayyana mutuwar tsohon hafsan sojin a matsayin babban rashi ga iyalansa da kuma Najeriya baki ɗaya.

Rabe.
Tsohon mai magana da yawun hedkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar Hoto: DHQ Nigeria
Source: Twitter

Ana ci gaba da ƙoƙarin ceto matarsa

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kubutar da Hajiya Amina, amma sun ƙi bayyana cikakken bayani ko lokacin da ake sa ran samun nasara a aikin.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyuka a yankunan da ake zargin masu garkuwar na boye da ita domin kubutar da ita, kamar yadda DCL Hausa ta kawo.

DHQ ta yi alhinin rasuwar Rabe Abubakar

A baya, kun ji cewa Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana alhini da jimaminta kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu a hannun 'yan bindiga.

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran DHQ, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar, rundunar sojin Najeriya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokan aikinsa da daukacin ’yan Najeriya.

DHQ ta jaddada cewa mutuwar Janar Rabe Abubakar za ta ƙara musu kaimi a ƙudurin yaƙar ta’addanci da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262