An Gano Mutumin da Ya Taimakawa Adeyemi a Badakar Hukumar Bogi Ta PFIPC
- Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta amince cewa ofishinta bai yi cikakken bincike ba kafin amincewa da wasu takardu
- Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya ce wani jami’insa ne ya karkatar da wata takarda da aka aika ga Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa
- Kwamitin Majalisar Wakilai ya ce an yi amfani da takardun nadin mukamai da na gwamnati na bogi wajen samun amincewar hukumar PFIPC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sababbin bayanai sun bayyana a ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026 yayin binciken da Majalisar Wakilai ke yi kan Hukumar PFIPC da ake zargin an kafa ba bisa doka ba.
Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta amince cewa ofishinta bai gudanar da cikakken bincike ba kafin ya amince da wasu muhimman takardu da suka shafi hukumar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya dora alhakin karkatar da wata takardar gwamnati kan wani jami’insa, wanda ake zargin aikinsa ya taimaka wajen ci gaba da gudanar da tsarin bogin.
Sababbin bayanai kan PFIPC
Ofishin Akanta Janar ya bayyana cewa wani jami’insa mai suna Bello Abdullahi ne ya karkatar da wata takarda da aka aika ga Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa.
Daraktan Sashen Kula da Harkokin Kudi na Ayyukan Tarayya a Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Joshua Luka, ya bayyana yadda aka bai wa hukumar da ake zargi lambar gudanarwa.
Yadda aka bayar da lambar gudanarwa
Luka ya ce ofishin ya karbi wata bukata da ta yi kama da wadda ta fito daga Fadar Shugaban Kasa, sannan ya aika da amsarsa ga Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa maimakon hukumar kai tsaye.
“A matsayin wani bangare na binciken da muka yi, mun aika da lambar gudanarwar ga Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, ba ga hukumar ba. Manufar ita ce idan ba gaskiya ba ce, za a gano komai.”
- Joshua Luka
Sai dai kwamitin ya soki wannan bayani bayan hujjoji sun nuna cewa takardar ba ta kai ga Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa ba, illa dai Adeyemi ne ya karbe ta, TheCable ta kawo labarin.
Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya kuma ce binciken ya tabbatar da cewa Sashen Gudanarwa da Ayyukan Tallafi da ya bayyana a cikin takardun bai wanzu a Fadar Shugaban Kasa ba.
Ya soki jami’an Ofishin Akanta Janar saboda barin wanda ake zargi ya karbi wata takardar gwamnati da aka aika ga wani ofishin gwamnati daban.
Jami’i ya amince da bai wa Adeyemi takarda
Luka ya dage cewa matsalar ta samo asali ne daga kuskuren mutum guda, ba gazawar hukuma baki daya ba.
“Matsalar da ke nan ba gazawar ofishi ba ce, kuskuren mutum ne. An ba wani mutum aikin kai wannan takarda ga Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa, amma ba a kai ta can ba.”
- Joshua Luka

Source: Facebook
Da aka matsa masa ya bayyana sunan wanda ke da alhakin lamarin, Luka ya ambaci Bello, wanda ke zaune a layin baya a Dakin Sauraron Kara na 028.
Bello ya amince cewa ya bai wa Adeyemi takardar, amma Gagdi ya dakatar da shi yayin da yake kokarin bayyana yadda lamarin ya faru.
'Yan sanda sun kasa kawo Adeyemi
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta kasa kawo Adeniyi Adeyemi gaban Majalisar Wakilai.
Sufeto-Janar na 'yan sanda ya bayyana cewa ba a kawo shugaban na hukumar bogi ta PFIPC ba ne saboda umarnin da kotu ta bayar.
Asali: Legit.ng


