Hatsabiban 'Yan Bindiga 18 da Aka Kashe a 2025 da Tasirin hakan ga Tsaron Arewa
A cikin shekarar 2025, hukumomin tsaro sun samu nasarar kame da kashe fitattun ‘yan bindiga da suka addabi yankunan Arewacin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wannan ci gaban ya kawo sauyi a fannin tsaro, musamman a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, da Kaduna, inda hare-haren ‘yan bindiga suka yi kamari.

Asali: Twitter
Jagororin 'yan bindiga da aka kashe a 2025
A wannan rahoto na musamman, za mu yi duba kan manyan ‘yan bindigan da aka kama ko aka kashe a farkon 2025 da yadda hakan ya shafi matsalar tsaron Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Kachalla Na Faranshi
Dakarun Operation Fansan Yanma sun kashe fitaccen dan bindiga, Kachalla Na Faranshi, da yaransa yayin sumame a dazukan Zurmi, jihar Zamfara.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe Kachalla Na Faranshi ne bayan musayar wuta da sojoji a dajin Dutsen Kura, kusa da Mashema.
Mun ruwaito cewa, Na Faranshi, wanda dan asalin garin Shirgi, da ke Maradi, kasar Nijar ne, ya fara sana'ar fataucin dabbobi kafin shiga ta’addanci da safarar makamai.
An ce sansaninsa ya na Dutsen Kura, yankin Kudu maso Yammacin Mashema da ke a karamar hukumar Zurmi, inda ya addabi al’umma.
2. Dogo Saleh
Rundunar ‘yan sanda ta ƙasar nan ta samu babban nasara wajen murƙushe Dogo Saleh, ɗan ta’adda da ke addabar Abuja da yankunan kewaye.
Binciken hukuma ya tabbatar da cewa matashin dan bindigar ya jagoranci hare-hare da garkuwa da mutane a Kaduna, Abuja da wasu yankuna.
Rahoton Legit.ng Hausa ya nuna cewa jami’an tsaro sun samu sahihan bayanai a kansa, inda suka bi sawunsa har suka cafke shi a Dajin Gidan Abe, kafin ajalinsa.
3. Shekau
Mun ruwaito cewa an hallaka wani shahararren ɗan fashi da ya yi wa kansa lakabi da Shekau bayan farmakin da wata gungun 'yan bindiga suka masa a Kachia, jihar Kaduna.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani dan bindiga Shumo, da ke garin Ragadada, a Buruku ta Birnin Gwari, ya farmaki Shekau a wani harin ramuwar gayya.
Rahotanni sun bayyana cewa Shekau ya taba kwace makaman Shumo tare da kashe mayaƙansa, wanda ya jawo kai masa farmakin ramuwar gayya.
Harin, wanda aka kai a ranar 5 ga Maris, 2025, ya yi sanadin mutuwar Shekau tare da wasu daga cikin manyan abokansa.
4. “Baƙo-baƙo”
An hallaka Baƙo-baƙo, shugaban ƙungiyar 'yan bindiga, tare da mayaƙansa a wani samame da jami’an tsaro suka kai a dajin Batsari da ke Katsina.
Majiyoyin tsaro sun ce sojoji, ‘yan sanda, NSCDC da dakarun tsaron Katsina, sun tsara harin cikin hikima, inda suka afka wa 'yan bindigar da dare.
A musayar wuta mai tsanani, Baƙo-baƙo da mukarrabansa sun sha kashi bayan da jami’an tsaro suka rinjaye su da dabaru, har suka kashe dan ta'addar.
Baƙo-baƙo ya dade yana addabar al’umma da hare-hare da garkuwa, kuma jami’an tsaro sun dade suna bincike kan ayyukansa a jihar Katsina.
5. Dan bindiga, Na’ballo
Mun ruwaito cewa an hallaka Na’ballo, fitaccen jagoran ‘yan bindiga mai alaka da Ado Aleiro, a wata mummunar arangama tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga.
Na’ballo ya kasance babban jigo a harkar ta’addanci, inda yake jagorantar hare-hare daga maboyarsa a Takulawa, karamar hukumar Tsafe.
Madarar bayanai sun tabbatar da cewa Na’ballo ya rasu a rikicin cikin gida da ya mamaye kungiyoyin ƴan bindiga a yankin.
6. Kachalla Dan Lukuti
An ruwaito mutuwar Kachalla Dan Lukuti, fitaccen shugaban ‘yan bindiga da ke jagorantar hare-hare a Zamfara da Katsina, bayan wata cuta mai ban mamaki.
Majiyoyi sun bayyana cewa ya kamu da rashin lafiya mai sarkakiya, wanda ta sa shi kakkarwa, kai harin cizo, tare da yin kururuwar da ta yi kama da haushin kare.
'Yan bindigar da ke cikin kungiyarsa sun firgita da halin da ya shiga, inda suka gudu suka bar shi, ba tare da iya taimakonsa ba.

Kara karanta wannan
Jigawa: Amarya ta watsawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi, ta zama silar ajalinta
A karshe, Kachalla Dan Lukuti ya yi mutuwar wulakanci sakamakon cutar, abin da ya jefa mabiyansa cikin rudani.
7. Kachalla Gwammade, Kachalla Shehu

Asali: Twitter
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar da kisan Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu, shahararrun jagororin ‘yan bindiga a Zamfara.
A cewarsa, dakarun Operation Fansan Yanma a karkashin atisayen "Show No Mercy", sun kashe su a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, a kauyen Ruwan Dawa, Maru.
Bayan Gwammade da Shehu, an kuma kashe mayakansu hudu, yayin da sojoji suka kwace babura uku da makamai masu yawa, kamar yadda muka ruwaito.
8. Hatsabiban 'yan bindiga sun mika wuya
Shahararrun shugabannin ‘yan bindiga da suka addabi Batsari, Safana, da Jibia a Jihar Katsina sun mika wuya tare da ajiye makamansu bayan matsin lamba daga dakarun soja.
Daga cikin wadanda suka mika wuya akwai Abu Radda, Umar Black, Abdullahi Lankai, Jijjige, da Dabar Musa Dan Gandu, dukkansu daga yankin Jibia.
Bincike ya nuna cewa hare-haren sojoji da suka tsananta a yankin sun tilasta wa wadannan ‘yan bindiga yin saranda da neman zaman lafiya.
9. Hamisu Saleh
Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun hallaka shahararren jagoran ‘yan ta’adda kuma mai garkuwa da mutane, Hamisu Saleh, da aka fi sani da “Master”, a Barkin Ladi, Plateau.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kaddamar da samamen da ya yi ajalin Hamisu ne a ranar 11 ga Fabrairu, 2025, a kokarin dakile ayyukan ta’addanci a yankin.
Mun ruwaito cewa an taba kama Saleh a Disambar 2024 saboda hare-hare da sace mutane a Barkin Ladi, amma daga bisani ya sake fitowa ya ci gaba da ta’addanci.
10. Kamilu Buzaro
Dakarun hadin gwiwa, na sojojin Brigade 17 da rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji sun hallaka shahararren dan ta’adda, Kamilu Chiroma (Buzaro), a Katsina.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe Buzaro tare da wasu daga cikin yaransa a Dutsen Dargaza, gundumar Maidabino B, karamar hukumar Danmusa, a ranar 17 ga Fabrairu.
Bayanai daga masu leƙen asiri sun nuna cewa an aiwatar da farmakin ne bisa sahihan bayanan sirri, wanda ya ba sojoji damar kai mamaya cikin nasara.
Harin sama ya yi matukar illa ga ‘yan ta’addan, inda aka hallaka yawancin mayaƙan Buzaro tare da rusa mafakarsu.
11. An kama mai sayarwa Bello Turji makamai
Jami’an tsaro sun cafke shahararren dillalin makamai, Hamza Suruddubu, a Karamar Hukumar Isa, Jihar Sokoto, wanda ake zargi da samar da makamai ga ‘yan ta’adda.
Mun ruwaito cewa, Hamza Suruddubu, mazaunin Gabashin Sokoto, yana jigilar makamai daga Zamfara zuwa mafakar ‘yan ta’adda a yankin.
Ana zargin yana bai wa shahararrun ‘yan ta’adda kamar Bello Turji, Boka, da Halilu Buzu makamai don kai hare-hare.
Bincike ya tabbatar da cewa ba wai makamai kadai yake samarwa ba, har da kayan abinci da babura ga kungiyoyin ‘yan ta’adda.
12. Sojoji sun ragargaji tawagar Kachalla Haru
Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta kai hare-haren sama kan sansanonin ‘yan bindiga a Gabashin karamar hukumar Shinkafi, inda ta hallaka da dama tare da rushe maboyarsu.
Jaridar PM News ta rahoto cewa an kai farmakin ne a dajin Katsira, inda Kachalla Haru ke fakewa, tare da dajin Fakai, wuraren da ‘yan ta’adda ke buya.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an hallaka da dama daga cikin 'yan bindigar a wannan harin, tare da lalata kayayyakin abinci, da kayayyakin aiki.
13. Sojoji sun cafke fitattun 'yan bindiga a Filato
Dakarun Operation Safe Haven sun cafke manyan masu garkuwa da mutane biyu a Barkin Ladi, a wani samamen sirri da suka kai
Wannan na zuwa ne yayin da aka gudanar da Operation Golden Peace a Lugere Sho, Barkin Ladi, a ranar 24 ga Fabrairu da misalin karfe 2:20 na rana.
Samamen ya biyo bayan sahihin bayani da aka samu daga wani dan bindiga da aka kama a ranar 22 ga Fabrairu, inda aka sake cafke wani mai garkuwa a kauyen Kwok.
A yanzu haka dai sojoji na ci gaba da tsare shi, inda yake bayar da bayanai masu muhimmanci kan hare-haren da suke kaiwa a Filato da Nasarawa.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu
14. Kachallah Hassan Nabamamu
Dakarun Operation Fansan Yanma sun kashe shahararren ɗan bindiga Kachallah Hassan Nabamamu, wanda aka fi sani da Hassan Dantawaye.
Sojoji sun kashe Kachalla Nabamumu ne yayin da ya yi yunkurin tserewa da kwace bindiga daga hannun soja yayin jigilar sa zuwa Gusau, jihar Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an cafke Nabamamu, wanda ya dade yana addabar yankunan Tsafe da Mada, bayan wani kazamin faɗa a ranar 27 ga Fabrairu, 2025.
Yayin da ake kan hanyar kai shi Gusau a safiyar 28 ga Fabrairu, ya yi kokarin farmakar soja da nufin tserewa, lamarin da ya sa aka harbe shi nan take.
15. Fitattun 'yan bindiga sun mika wuya a Katsina
Shahararren ɗan bindiga Abu Radde da yaransa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro a Jihar Katsina, tare da sakin mutane goma da suka yi garkuwa da su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Abu Radde, Audu Lankai, Ori, Gila, Adamu Gurbi, Nawagini, Umar Black, Margyal da Aloda sun nemi sulhu ta hanyar tattaunawa da jami’an tsaro.
A matsayin alamar sadaukarwa, ‘yan bindigar sun miƙa bindigogi AK-47 guda biyu ga dakarun soji, tare da sakin waɗanda suka yi garkuwa da su.
An kai waɗanda aka ceto asibiti domin duba lafiyarsu, yayin da hukumomi ke ci gaba da tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
16. Sojojin sun farmaki tawagar Yusuf Yellow
Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta kashe ɗaruruwan ‘yan bindiga a ƙaddamar da luguden wuta a mafakar shahararren ɗan bindiga Yusuf Yellow a Karamar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara.
Wani babban jami’in tsaro da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da cewa harin ya yi nasara sosai, inda aka hallaka ‘yan ta’adda da dama.
Legit Hausa ta rahoto cewa, an kaddamar da luguden ne bisa cikakken bayanan sirri, wanda ya kai ga kawar da adadi mai yawa na ‘yan ta'addar.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da mutuwar Yusuf Yellow ba, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sa ido don tantance tasirin farmakin.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda
17. Shugaban Lakurawa, Maigemu
Dakarun hadin gwiwa na jami’an tsaro da ‘yan sa-kai sun kashe shahararren shugaban ‘yan bindiga, Maigemu, a karamar hukumar Arewa, jihar Kebbi.
Mun ruwaito cewa an kashe Maigemu ne a garin Kuncin Baba bayan wata mummunar arangama da jami’an tsaro a yankin mai wahalar shiga.
Wannan nasara na zuwa ne mako guda bayan Gwamna Nasir Idris ya ziyarci Bagiza da Rausa Kade don jajanta wa al’umma kan kashe mutum shida da ‘yan bindiga suka yi.
18. Yusuf Gwamna
Dakarun Operation Fansan Yanma sun kashe shahararren ɗan bindiga, Yusuf Gwamna, a Dutsin-Ma, Jihar Katsina, bayan mummunan arangama da ‘yan ta’adda.
Rahoton da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa sojoji hallaka wasu ‘yan bindiga da dama a harin da suka kai.
Yusuf Gwamna ya dade yana addabar al’ummar Katsina da makwabtanta, inda yake jagorantar hare-hare da garkuwa da mutane.
Kashe Yusuf Gwamna ya zama babbar nasara a yaki da ‘yan bindiga, yayin da al’umma ke fatan dawowar zaman lafiya a yankin.
19. Yellow Aboki
Dakarun da ke gudanar da fatattakar ‘yan bindiga a Zamfara sun kashe Yellow Aboki, shahararren ɗan bindiga kuma aminin Hassan Bamamu da aka kashe kwanan nan.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa sojoji sun hallaka Yellow Aboki a Arewa maso Yammacin Tsafe, yayin samamen Operation Fansan Yanma.
Harin na zuwa ne makonni bayan kashe Bamamu, wanda ya kasance babban kwamandan ‘yan ta’adda a yankin.
An rahoto cewa Yellow Aboki ya dade yana ƙoƙarin karɓe ragamar ayyukan ta’addanci bayan mutuwar Hassan Nabamamu.
20. Shehu Kwale
Dakarun Operation Fansan Yanma sun kashe Shehu Kwale, shahararren ɗan bindiga kuma aminin Dan Ishu, a wani samame da suka kai kusa da Mararrabar Kyaware, jihar Zamfara.
Majiyoyi sun shaida cewa dakarun sun farmaki ‘yan ta’addar a ranar 10 ga Maris, suka hallaka da dama daga cikinsu.
Shehu Kwale, wanda ya yi kaurin suna a kai hare-haren rashin imani, ya na cikin waɗanda aka kawar a harin.
Bincike ya nuna cewa Shehu Kwale ɗa ne ga wata mata, Hajiya Dudu Mainono, mazauniyar karamar hukumar Tsafe.
21. Kachallah Babangida
Dakarun sojin Operation Fansan Yanma sun ƙara matsa kaimi a Kaura Namoda, Zamfara, inda suka kashe shahararren ɗan bindiga Kachalla Babangida da wasu da dama.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, farmakin da aka kai a ranar 10 ga Maris, 2025, ya samu tallafi daga rundunar sojin saman Najeriya.
Dakarun sun kai samame sansanin Dan Sa'adi da safe, suka fafata da ‘yan bindiga kafin su yi nasara a harin haɗakar jiragen yaki da na sojojin kasa .
Rahotanni sun tabbatar da kashe Kachalla Babangida, rushe sansanoni, da lalata makaman ‘yan ta’adda a yankin.
22. Kachalla Dogo Idin Madu
Hadakar dakarun tsaro a Zamfara sun dakile harin ramuwar gayya na ‘yan bindiga a Mada, Gusau, inda suka kashe Dogo Idin Madu da wasu ‘yan ta’adda.
Majiyoyi sun shaida cewa ‘yan bindiga sun farmaki garin da safiyar Laraba, suna kokarin mayar da martani kan hare-haren da jami’an tsaro suka kai masu a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya
Sai dai dakarun Operation Fansan Yamma tare da Askarawa sun fatattaki maharan, suka kashe da dama, ciki har da Dogo Idin Madu, wanda aka dade ana nema ruwa a jallo.
23. Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina
Jiragen yakin Operation Fansa Yamma sun kai farmaki kan maboyar ‘yan bindiga a Unguwar Goga, da ke Faskari, a jihar Katsina, inda suka ragargaza sansanonin Gero (Alhaji) da Alhaji Riga.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kai harin ne da safiyar ranar 13 ga Maris, kuma ya lalata sansanonin biyu, kamar yadda Legit.ng Hausa ta ruwaito.
A kalla ‘yan bindiga 19 sun mutu a farmakin, yayin da ake kyautata zaton wasu sun hallaka a tsaunukan Ruwan Godiya, amma ba a tantance yawan su ba.
24. Abdullahi Snu (Honor) ya bakunci lahira
Dakarun hadin gwiwa na sojoji da ‘yan sanda sun yi nasarar kashe Abdullahi Snu, wanda aka fi sani da "Honor", fitaccen mai garkuwa da mutane da aka dade ana nema a Akwanga.

Kara karanta wannan
Sarkin Sasa: Awanni da birne shi, an sanar da sabon basarake da zai maye gurbinsa
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa an aiwatar da farmakin ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar 14 ga Maris, 2025, bayan samun sahihan bayanai.
An kashe wanda ake nema yayin da yake kokarin tserewa, inda aka kwato bindiga kirar Ingila da harsasai 12 daga gare shi.
26. Kachalla Dogo Isah
Shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Dogo Isah, ya mutu bayan artabu da wani gungun ‘yan bindiga a dajin Kachia, jihar Kaduna, a ranar 7 ga Janairu, 2025.
Bayanan sirri sun nuna cewa Dogo Isah da yaransa sun kai farmaki don kwace shanu daga sansanin tsohon dan bindiga Kachalla Musa, lamarin da ya haddasa fada.
Dogo Isah, wanda ya addabi Kachia da Kajuru, shi ne dan uwa ga Tukur Sharme, wani dan bindiga da aka kashe a rikicin cikin gida a 2024.
A rikicin, Dogo Isah da wasu mutum biyu daga kungiyarsa sun mutu bayan musayar wuta da dakarun Kachalla Musa a dajin Kachia.
Tasirin kisan 'yan bindiga ga tsaron Arewacin Najeriya
Yayin da ake ci gaba da fatattakar ‘yan bindiga da kuma ragargazar sansaninsu, akwai alamun cewa matakan tsaro na haifar da gagarumin sauyi a yankin Arewa.
Yawan kashe-kashen shugabannin ‘yan bindiga da rushe sansaninsu na rage karfinsu da kuma rage yawan hare-haren da suke kaiwa kan al’umma.
Duk da haka, masana tsaro na bayyana bukatar karin dabaru na tsaro, tare da hadin gwiwar al’ummomi da hukumomi don tabbatar da cewa an kawo karshen matsalar gaba daya.
Sojoji sun gano maboyar Bello Turji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar sojojin Najeriya ta ba da tabbacin cewa ana bibiyar Bello Turji, kuma za a kawar da shi nan ba da jimawa ba.
Manjo Janar Emeka Onumajuru, babban daraktan ayyuka a hedkwatar tsaro (DHQ) ya bayyana cewa suna da masaniya kan inda Bello Turji yake a halin yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng