Na’ballo: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Shugaban Ƴan Bindiga, Yaran Bello Turji Sun Tsere
- Na’ballo, shahararren shugaba na ƴan bindiga ya gamu da ajalisan a wata arangama da sojojin Najeriya a ƙaramar hukumar Tsafe
- Haka kuma, 'yan sojoi sun kashe wasu 'yan bindigar Fulani takwas da suka kai kan wata mota tsakanin garin Kucheri da Magazu
- Wannan na zuwa ne yayin da aka hango magoya bayan Bello Turji suna gudun ceton rai da neman mafaka a yankin Garsa/Kadanya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wani shahararren shugaban ƴan bindiga, Na’ballo, wanda aka ce na hannun daman Ado Aleiro ne.
Rahoto ya nuna cewa kasurgumin dan ta'adda, Na'ballo ya gamu da ajalinsa a yayin wata arangama mai zafi da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Asali: Twitter
An kashe shugaban 'yan bindiga, Na'ballo
Mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya sanar da hakan a shafinsa na X, yana mai cewa mutuwar Na'ballo sauki ne ga mazauna yankin Takulawa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na’ballo dai ya kasance hatsabibi kuma mai matuƙar ƙarfi a cikin ƴan bindiga, wanda ya shahara a gabashin Takulawa, da ke ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
Madarar bayanai sun tabbatar da cewa Na’ballo ya rasu a rikicin cikin gida da ya mamaye kungiyoyin ƴan bindiga a yankin.
Mutuwar Na'ballo na zuwa ne yayin da wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton cewa Fualni ne suka kai wa direban mota hari tsakanin ƙauyukan Kucheri da Magazu.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 8 a Zamfara
Sai dai direban motar ya samu nasarar tsira daga harin kuma ya kai rahoton ayyukan 'yan bindigar ga sojoji.
A cikin gaggawa, rundunar sojoji ta yi nasarar kashe dukkanin ƴan bindigar takwas da suka kai harin, ba tare da wani rauni ga fararen hula ba.
A wannan gabar ne aka ji cewa magoya bayan shugaban 'yan bindiga, Bello Turji suna canza wurin ɓoyarsu zuwa wata sabuwar mafaka a yankin Garsa/Kadanya.
Yaran Bello Turji sun fara gudun ceton rai
Majiyoyi sun shaida cewa an lura da motsin ƴan bindigar tsakanin ranar 19 da 20 ga Janairu, daga ƙarfe 4:45 na yamma zuwa 7:00 na safe.
A tsakanin wadannan lokuta ne aka ce magoya bayan Turji sun wuce ta garuruwan Galadi, Damaga, Rudunu da Danbenchi domin zuwa sabuwar makafarsu.
An ce Jummo Smally, wanda ya kasance abokin hamayyar Turji, shi ne ke riƙe da sabuwar mafakar 'yan bindigar.
Wannan na zuwa ne yayin da sojojin Najeriya suka tsananta kai hare-hare kan sansanonin 'yan ta'adda a Zamfara, wanda ya tilasta wa Turji da magoya bayansa guduwa.
Bello Turji ya kafa sabon sansani a Zamfara
Tun da fari, mun ruwaito cewa Bello Turji ya kafa sabon sansani a Dajin Dutsi da Yan Buki bayan rasa dansa da mummunan asara a hare-haren sojoji.
Rahoto ya bayyana cewa Turji ya mayar da sansanin matsayin matattarar ‘yan ta’adda da kuma kula da wadanda aka raunata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng