Tsohon Hadimin Atiku Ya Girma, Ya Samu Tikitin Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027
- Tsohon hadimin Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADP a babban zaben 2027 da ke tafe
- Ambasada Aliyu Bin Abbas ya zama dan takarar ADP ne bayan shugabanni da magoya bayan sun tabbatar da shi a safiyar yau Asabar
- Aliyu ya bayyana cewa takararsa tana wakiltar muradin matasan Najeriya masu neman sababbin shugabanni masu gaskiya da hangen nesa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADP ta zaɓi Ambasada Aliyu Bin Abbas a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027.
An tabbatar da nasarar Abbas ne a safiyar Asabar yayin babban taron jam'iyyar na ƙasa da aka gudanar a birnin Abuja, inda ya samu amincewar wakilan jam’iyyar ta ADP.

Source: Twitter
Aliyu Bin Abbas ya samu tikitin ADP

Kara karanta wannan
Peter Obi ko Kwankwaso: NDC ta shirya tsaida 'dan takarar shugaban kasa a zaben 2027
Fitowar Aliyu Bin Abbas a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ya sa ya zama ɗaya daga cikin manyan ’yan siyasar Arewa da za su iya kece raini a babban zaben 2027.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Okpani Jacob Onjewu Dickson, ya fitar, ya ce an sanar da sakamakon zaɓen ne da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Asabar.
Sanarwar ta ce magoya baya da wakilan jam’iyyar ADP sun yi murna matuƙa bayan tabbatar da nasarar Aliyu a wajen taron.
Yadda bn Abbas ya rabu da Atiku Abubakar
Aliyu Bin Abbas ya taɓa zama hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda shi ma yanzu yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC.
Sai dai sanarwar ta jaddada cewa takarar Abbas ba ta da alaƙa da Atiku ko wata tsohuwar ƙungiyar siyasa.
Ta ce:
"Domin kawar da duk wata shakka, Ambasada Aliyu Bin Abbas ya shiga wannan takara ne bisa cancantarsa kuma a karkashin dandamali mai cikakken ’yanci.
"Duk da cewa ya taɓa zama kusa da Atiku Abubakar a siyasa, wannan alaƙa ta ƙare sama da shekaru biyu da suka gabata bayan bambance-bambancen siyasa da suka shiga tsakaninsu."

Kara karanta wannan
Jam'iyyar NDC ta jawo Kabiru Marafa, ta ba shi tikitin takarar gwamnan Zamfara a 2027
Sanarwar ta ƙara da cewa takararsa tana wakiltar muradin matasan Najeriya masu neman sababbin shugabanni masu gaskiya da hangen nesa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Source: Facebook
Abbas ya yi alƙawarin kawo sauyi a Najeriya
Da yake jawabi bayan samun tikitin takarar, Aliyu Bin Abbas ya bayyana nasararsa a matsayin farkon sabon babi na shugabanci a Najeriya.
Ya ce:
"Wannan ba nasara ce ta siyasa kawai ba. Alama ce ta fitowar sabon ƙarni na shugabanni masu ƙudurin farfaɗo da Najeriya, inganta tattalin arziki da kuma bai wa matasa dama."
Mace za ta kara da Bola Tinubu a 2027
An ji cewa jarumar fina-finai a Najeriya, Esther Okereke ta samu nasarar zama 'yar takarar shugaban kasa ta jam'iyyar NRM a zaben 2027.
An tabbatar da Jaruma Okereke a matsayin ‘yar takarar jam’iyyar ne ta hanyar maslaha yayin zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar Juma’a.
Shugaban jam’iyyar NRM na kasa, Chinedu Obi, ya bayyana cewa Esther Okereke ce kadai ta cika dukkan sharuddan tantance ‘yan takara da jam’iyyar ta gindaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng