An Yi Rashi: Babban Malamin Addinin Musulunci a Kwara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Rashi: Babban Malamin Addinin Musulunci a Kwara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An yi babban rashi a jihar Kwara bayan wani babban malamin addinin Musulunci ya yi bankwana da duniya a karshen shekarar Musuluncin bana
  • Khalifatul-Adabiyah, Ash-Sheikh Abdulqodir Muhammad Kamaludeen Al-Adabiy ya yi bankwana da duniya a ranar Juma'a, 29 ga watan Mayun 2026
  • Marigayin ya kasance kasance ɗa ga marigayi Sheikh Muhammad Kamaldeen Al-Adaby, wanda shi ne ya kafa gidauniyar Ansarul Islam Society of Nigeria

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Khalifatul-Adabiyah, Ash-Sheikh Abdulqodir Muhammad Kamaludeen Al-Adabiy, ya rigamu gidan gaskiya.

Malamin addinin, wanda ɗa ne ga fitaccen masanin ilimin Musulunci, Sheikh Muhammad Kamalud-deen, ya rasu ne a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 29 ga watan Mayun 2026.

Malamin addinin Musulunci ya rasu a Kwara
Malamin addinin Musulunci a Kwara, marigayi Abdulqodir Muhammad Kamaludeen Al-Adabiy Hoto: Muneen Olupejobi Adegoke, Idris Abdulganiy Yinka
Source: Facebook

A cewar rahoton jaridar The Punch, wani shahararren malami a Ilorin, Shaykh Abdul Fatah Aribidesi, ya ce marigayin ya rasu ne a garin Ilorin.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Gwamna Buni ya yi wa musulmi nasiha, ya tabo rayuwar Annabi Muhammad SAW

Malamin addinin Musulunci ya rasu a Kwara

Sarkin Ilorin kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kwara, Mai-Martaba Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari CFR, ya nuna alhininsa game da rasuwar Khalifatul Adabiyyah.

Mamacin, wanda shi ne babban ɗa namiji na fari da ya rage a raye ga Sheikh (Dr.) Muhammad Kamaludeen Al-Adaby, marigayi Muftin kasa na farko na Ilorin, ya rasu ne ranar Juma'a a Ilorin.

Alhaji Sulu-Gambari, a cikin wani saƙon ta'aziyya da mai magana da yawunsa, Dr. Abdulazeez Arowona, ya fitar, ya bayyana "lamarin a matsayin wani babban rashi ga al'ummar Masarautar Ilorin da ma ɗan adam baki ɗaya."

An yi ta'aziyya kan rasuwar malamin

Sarkin ya kuma nuna alhininsa kan rasuwar mahaifin Alhaji Uthman Jagunmo, shugaban kungiyar ci gaban matasan masarautar Ilorin (IEYDA) na kasa kuma Jagunmon Ilorin, wato Alhaji Alabi Jagunmo.

Ya lura cewa duka rasuwar mutane biyun sun kasance babban rashi mai raɗaɗi ga Masarautar Ilorin, kuma ya ce ya miƙa wuya kacokan ga hukuncin Allah Maɗaukakin Sarki.

Kara karanta wannan

"Ku yi wa Najeriya addu'a" Ministan Tinubu ya aika sakon barka da Sallah

Malamin addinin Musulunci ya rasu a Kwara
Marigayi Sheikh Abdulqodir Muhammad Kamaludeen Al-Adabiy Hoto: Muneen Olupeji Adegoke
Source: Facebook

An yi masu addu'ar samun rahama

Alhaji Sulu-Gambari ya roƙi Allah cikin madaukakiyar rahamarSa da Ya ji kan su duka biyun, wato Khalifatul Adabiyya da Jagunmon Ilorin.

Marigayin ya kasance ɗa ga marigayi Sheikh Muhammad Kamaldeen Al-Adaby, wanda shi ne ya kafa gidauniyar Ansarul Islam Society of Nigeria (wanda aka fi sani da Azumratul Adabiyyah Al-Kamoliyyah).

Sheikh Muhammad Al-Adaby yana da kimanin shekaru 98 zuwa 100 a duniya sa'ilin da ya rasu a shekarar 2005.

Alhaji daga Najeriya ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa daya daga cikin Alhazan Najeriya da ke gudanar da aikin hajjin 2026 ya riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiyya.

Alhajin dan Najeriya wanda ake kyautata zaton dan asalin jihar Bauchi ne ya rasu a kasa mai tsarki a Muzdalifah.

An ga jami’an tsaron Saudiyya da ma’aikatan lafiya na gaggawa suna kwashe gawar mamacin daga wurin da ya rasu da sanyin safiya bayan mahajjata sun kwana suna tafiya daga Arafa zuwa Muzdalifah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com