Bayan Watsi da Jam’iyyar APC, Dan Nasir El Rufai Ya Tashi da Tikiti a ADC
- Dan majalisar tarayya daga jhar Kaduna, Bello El-Rufai ya lashe tikitin kujerar majalisar wakilai ta ADC mai wakiltar Kaduna ta Arewa
- Majiyoyi sun tabbbatar da cewa dan tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya samu nasarar ba tare da hamayya ba bayan samun ƙuri'u 7,727
- Ɗan majalisar ya gode wa shugabannin jam’iyya, wakilai da magoya baya bisa amincewa da suka nuna masa a zaɓen fidda gwani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Dan tsohon gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai, ya samu nasara bayan gudanar da zaben fitar da gwanin ADC a Kaduna.
Dan majalisar tarayya, Bello ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ADC ba tare da samun wani abokin hamayya ba.

Source: Facebook
A wata sanarwa da ya fitar a Facebook a jiya Juma'a 29 ga watan Mayun shekarar 2026, Bello ya ce ya samu ƙuri’u 7,727 a zaɓen.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar NDC ta jawo Kabiru Marafa, ta ba shi tikitin takarar gwamnan Zamfara a 2027
Bello El-Rufai ya yi godiya ga shugabannin ADC
Ya gode wa shugabannin jam’iyyar, wakilai, masu ruwa da tsaki, magoya baya da al’ummar Kaduna North saboda amincewa da goyon bayan da suka nuna masa.
Bello ya bayyana cewa cikin shekaru uku da suka gabata ya yi aiki tuƙuru tare da tawagarsa domin wakiltar al’ummar mazabarsa yadda ya kamata.
Ɗan majalisar ya ce lokacin da yake APC bai taɓa hulɗa ko tallafa wa jam’iyyun adawa ba, duk da rade-radin da ake yadawa.
Ya ce:
“Bari na yi bayani. Lokacin da nake cikin APC, ban taɓa hulɗa da jam’iyyun adawa ba. Ban taɓa ɗaukar nauyin su da kuɗi ba. Mahaifina ma ya san bai kamata ya nemi in yi hakan ba."

Source: Original
Bello ya yi alfaharin kasancewa a ADC
Bello ya bayyana cewa yanzu yana cikin ADC cikin alfahari, yana mai tabbatar da ce duk wanda ke da shakku cewa zai yi wa jam’iyyarsu yaƙin neman zaɓe da farin ciki, kuma sun san tarihin aikina, Bai tsoron kowa.

Kara karanta wannan
'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki
A madadin al’ummar Kaduna North, ya roƙon a isar musu da godiyata, ya ce waɗannan su ne mutanen da, duk da ƙoƙarinsu, da sun iya kayar da shi idan ba su janye takararsu ba, domin shi ya zo jam’iyyar ne a makare.
Ya ƙara da cewa yanzu yana cikin ADC da alfahari, kuma zai yi wa jam’iyyar yaƙin neman zaɓe da ƙwazo, yana mai cewa ba sa tsoron kowa.
Isah Ashiru ya samu takara a Kaduna
A wani labarin, an ji cewa tsohon dan majalisar tarayya daga Kaduna, Isah Ashiru Kudan ya samu tikitin takarar gwamna a jihar karkashin ADC mai hamayya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan ya biyo ne bayan zaben fitar da gwani da aka gudanar a fadin jihar inda ya samu dubban kuri'u.
Sai dai tsohon Kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna ya yi watsi da sakamakon zaben, yana mai cewa an tafka magudi da karkatar da kuri’u a wasu yankuna.
Asali: Legit.ng