Auren Gata: Ana Zargin Limami Ya Haɗa Yaransa Aure, An Bankado Wasu Badaƙaloli a Katsina

Auren Gata: Ana Zargin Limami Ya Haɗa Yaransa Aure, An Bankado Wasu Badaƙaloli a Katsina

  • Ana zargin wani limami a Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa da haɗa ’ya’yansa a matsayin amarya da ango domin cin gajiyar tallafin auren gata
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa akwai ma’auratan da aka sake ɗaura wa aure a cikin shirin domin samun tallafin gwamnatin jihar Katsina
  • An kuma samu ƙorafe-ƙorafe kan musayar sunaye, cire waɗanda aka tantance da kuma zargin sa hannun wasu ’yan siyasa a auren gatan gwamnatin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Wasu zarge-zarge masu tayar da hankali sun kunno kai bayan makonni uku da gudanar da auren gata da gwamnatin jihar Katsina.

Kara karanta wannan

"Ina tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo ya dura a kan gwamantin Abba

Gwamnatin a karkashin Umaru Dikko radda ta shirya auren gata inda aka ɗaura auren mutane 2,000 a ranar 9 ga Mayu, 2026.

Ana zargin badakala a auren gatan jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda Hoto: Dikko Umaru Rada
Source: Facebook

Binciken kwakwaf na jaridar Aminiya ya nuna cewa ana zargin wani limami a yankin Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa da aurar da wasu daga cikin ’ya’yansa ga junansu domin samun tallafin da gwamnati ta ware wa ma’aurata.

Dalilin gwamnatin Katsina na yin auren gata

Rahoton ya ce an yi hakan ne da nufin cin moriyar kuɗi da sauran tallafin da Gwamnatin jihar ta tanada a ƙarƙashin shirin.

An ƙaddamar da auren gatan ne domin rage matsalolin zamantakewa, musamman a tsakanin waɗanda matsalar tsaro ta shafa, marayu da kuma masu ƙaramin ƙarfi da ke son yin aure amma ba su da hali.

Tun da farko, Hukumar Hisba ta jihar ta gudanar da bincike tare da ba gwamnatin Gwamna Dikko Umar Raɗɗa shawarar ɗaukar nauyin irin wannan shiri.

Kafin ɗaurin auren, an gudanar da gwaje-gwajen lafiya da na ƙwayoyin halitta tare da horas da amaren da angwaye kan rayuwar aure. Haka kuma gwamnati ta ɗauki nauyin sadaki na N100,000 ga kowace amarya, tare da kayan ɗaki da jari bayan koyar da su sana’o’i.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi gargadi mai zafi kan zargin shirin amfani da addini a zaben 2027

Sai dai bayan kammala shirin, rahotanni sun fara bayyana kan yadda wasu suka yi amfani da damar wajen samun abin duniya.

Ana zargin badakaloli a auren Katsina

Fitaccen malamin addini, Dakta Aminu Yammawa, ya bayyana a wani karatu cewa wasu ma’aurata sun shiga cikin shirin duk da cewa tun farko suna tare a matsayin miji da mata.

Ana zargin har da ma'aurata a cikin wadanda suka shiga auren gata a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ake zargin an yi badaka a auren gata Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“Akwai waɗanda suka kira ni ta waya, mata ce da miji suke tambaya ta ko yaya matsayin aurensu yake a yanzu? Da ma ma’aurata ne, amma don su samu abubuwan da aka tanadar wa waɗanda za a yi wa auren, suka shiga tsarin aka sake ɗaura masu aure.”

Malamin ya kuma ce wani mutum ya shaida masa cewa yana da niyyar sakin matar bayan karɓar tallafin saboda ba shi da ikon ci gaba da riƙe ta.

Kara karanta wannan

'Yadda Tinubu ya sadaukar da komai domin ceto 'yan Najeriya daga halin kunci'

Sai dai wani basarake daga Ƙaramar Hukumar Katsina ya dora alhakin abin da ya faru kan wasu ’yan siyasa, yana mai cewa sun yi amfani da tasirinsu wajen saka mutanensu cikin shirin.

An shirya auren gata a Katsina

A baya, mun kawo labarin cewa Gwamnatin jihar Katsina tare da hadin gwiwar wata kungiyar sa-kai sun shirya gudanar da auren gata ga mutane da dama domin taimakon masu karamin karfi.

Rahotanni sun bayyana cewa an shirya gudanar da auren gatan ne ga maza da mata domin rage aikata ayyukan alfasha da tallafawa mutanen da ba su da halin yin aure a halin da tattalin arziki ke ciki.

A shirye-shiryen gudanar da auren gatan, an shirya taron karawa juna sani da horo ga masu shirin zama ma'auratan da kuma sauran tsare-tsare da za su taimaka wajen dorewar zaman auren.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng