Bayan Hallaka Jama'a da Karbe Kudin Fansa, Mugun 'Dan Ta'adda Ya Gamu da Karshensa
- Rundunar ‘yan sanda kasar nan ta samu gagarumar nasara wajen murkushe Dogo Saleh, shahararren ɗan ta'adda da ke addabar al’umma Abuja da kewaye
- Binciken ‘yan sanda ya nuna mugun matashin ya jagoranci hare-hare da garkuwa da mutane a wurare da dama, ciki har da Kaduna, Abuja da wasu yankuna
- Rahotanni sun bayyana cewa bayan jami’an tsaro sun samu sahihan bayanai a kansa ne sai suka bi sawu, har su ka cimmasa a dajin gidan Abe
- Bayan hallaka Dogo Saleh, an gano wasu muhimman kayayyakin aikata ta'adi irinsu bindigar AK-49, harsasai 60, da kudi da sun kai N3,000,000
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Rundunar ‘yan sanda ta birnin tarayya Abuja ta hallaka shahararren ɗan ta'adda, Salisu Mohammed wanda aka fi sani da Dogo Saleh.
Sun yi nasarar sada shi da Mahaliccinsa ne bayan wani gagarumin samame da aka kai domin dakile ayyukan gungun masu garkuwa da mutane a yankin.

Asali: Facebook
Vanguard News ta wallafa cewa rundunar ta ce mutuwar wannan shahararren ɗan fashi wanda ke addabar mazauna hanyar Kaduna - Lokoja - Enugu da Abuja babbar nasara ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama dan ta'adda a dajin gidan Abe
Daily Post ta wallafa cewa ‘yan sanda sun kai samame a ranar 3 ga watan Maris, 2025, bayan samun sahihan bayanai game da shigowar wasu ‘yan bindiga cikin Abuja.
Bayan bibiyar sawu, jami’an tsaro sun yi nasarar kama Salisu Mohammed, ɗan shekara 21, a dajin Gidan Abe yayin da yake kan hanyarsa zuwa ƙaramar hukumar Bwari a Abuja.

Asali: UGC
An bayyana Dogo Saleh, ɗan asalin Baban Saural, Chikun LGA, Kaduna a matsayin hatsabibin ɗan bindiga da ke aiki da shahararrun shugabannin ‘yan fashi a dajin Rijana, Kaduna.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka
Ya dade yana addabar jama’a tare da garkuwa da mutane akan manyan tituna domin karɓar kuɗin fansa masu yawa.
An kwato makamai daga dan ta'adda
'Yan sanda sun ce lokacin da aka yi masa kofar rago, Dogo Saleh ya yi ƙoƙarin tserewa tare da barin wasu kayansa, ciki har da bindigar AK-49 mai cazbi guda biyu da harsasai 60.
Haka kuma an samu kudi da yawansu ya kai N3,000,000 da ya samo daga garkuwa da bayin Allah da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Rundunar ‘yan sanda ta Abuja ta ce za ta ci gaba da farmakar ‘yan bindiga domin tabbatar da zaman lafiya a yankin da kewaye.
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 40
A wani labarin, kun ji cewa zaratan sojojin kasar nan tare da haɗin gwiwar Askarawan jihar Zamfara sun yi nasarar daƙile harin da ƴan ta'adda su ka kitsa kan bayin Allah.

Kara karanta wannan
Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigan sun shirya kai farmaki domin ramuwar gayya, bayan da dakarun sojoji su ka kashe ɗaya daga cikin manyan shugabanninsu, Sani Dan Garin Bawo.
Yayin da suka doshi garin, dakarun sojoji da ƴan sa-kai sun tare su, suka shiga fafatawa da musayar wuta, har ta kai a ƙarshe an samu nasarar hallaka akalla ƴan bindiga 40.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng