Ajali Ya Yi Kira: Hatsabibin Ɗan Bindiga, Shekau Ya Mutu yayin Arangama da Ƴan Ta'adda

Ajali Ya Yi Kira: Hatsabibin Ɗan Bindiga, Shekau Ya Mutu yayin Arangama da Ƴan Ta'adda

  • Wani daga cikin hatsabiban 'yan bindiga da yake kiran kansa da Shekau ya mutu a wajen wani kwanton-bauna
  • An ce Shekau ya mutu ne yayin hari da wasu gungun 'yan bindiga na adawa suka shirya a Kachia da ke jihar Kaduna
  • Majiyoyi sun ce dan bindiga, Shumo ya kai farmakin domin daukar fansa kan Shekau, wanda ya kwace makamansa
  • An kashe Shekau da wasu daga cikin yaransa a kwanton-bauna da aka kai masa ranar 5 ga Maris, 2025, a kogin Narewo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Wani fitaccen dan bindiga da ake kira Shekau, saboda mugun halinsa ya mutu yayin arangama da yan bindiga.

Majiyoyi sun ce an kashe shi a kwanton-bauna da wata gungiyar ‘yan bindiga da Shumo ke jagoranta ta shirya.

Kara karanta wannan

Bayan alkawarin gwamna kan miyagu, jami'an tsaro sun hallaka jagoran Lakurawa

An sheke fitaccen dan bindiga a Kaduna
Yan bindiga sun yi ajalin hatsabiban ɗan ta'adda da ake kira Shekau a Kaduna. Hoto: Legit.
Asali: Original

An tsinci gawar malamin coci da aka sace

Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa Shumo, wanda dan asalin Ragadada, Buruku ne a Birnin Gwari, ya kai farmakin domin ramuwar gayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun hallaka babban limamin cocin katolika da suka yi garkuwa da shi ranar Talata 4 ga watan Maris, 2025 a yankin Kauru a Kaduna.

Shugaban cocin a Kafanchan, Rabaran Jacob Shanet ya tabbatar da hakan ranar Laraba 5 ga watan Maris, 2025, ya roƙi matasa su kwantar da hankalinsu.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kaduna, Mansir Hassan ya ce sun tura dakaru yankin domin kamo waɗanda suka yi kisan.

Yadda aka yi arangama tsakanin yan bindiga

Hakan ya biyo bayan kwace makamansa da Shekau ya yi kuma ya kashe mayakansa da dama a baya.

An tattaro cewa yayin kwanton-baunar, Shekau da wasu daga cikin mukarrabansa sun mutu a harin da aka kai ranar 5 ga Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Ramadan: Direba ya murkushe sufetan ɗan sanda da ke bakin aiki a masallacin Abuja

An birne ‘yan bindigar da aka kashe ta hannun wasu da aka bayyana da Yellow Million da Baba Kusa.

Hatsabibin dan bindiga ya mutu yayin arangama da yan uwansa
An tabbatar da kisan wani fitaccen dan bindiga, Shekau a Kaduna. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Limami ya jagoranci sallar jana'izar 'dan bindiga

An tabbatar da cewa wani babban malamin addini ne daga kauyen Kabode a Kachia ya yi masa sallah.

Sai dai wasu yan Najeriya da dama sun kushe limamin da zai taimaka wurin birne dan ta'addan inda wasu ke zargin ko barazana aka yi masa.

Duk da haka an ce ayyukan ‘yan bindiga ya ragu a Kaduna sakamakon kokarin gwamnati da jami’an tsaro, cewar Daily Post.

An tabbatar cewa rikici tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga na karuwa tare da asarar rayuka da dama.

Sojoji sun hallaka yan bindiga a Kaduna

Mun ba ku labarin cewa dakarun sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane biyu a Jema’a da ke jihar Kaduna, bayan sun kai dauki don ceto fasinjoji da aka sace.

An kai farmakin ne a dajin Angwan Rimi inda sojoji suka kwato bindigar AK-47, harsasai takwas, wayoyi 10 da tsabar kudi N1,136,000.

Kara karanta wannan

An yi jina jina da 'yan banga suka gwabza kazamin fada da 'yan bindiga

Har ila yau, an ceto mutum uku da aka sace, ciki har da Mathew Ayemowa, Tunde Salam da Mustapha Mohammed, bayan artabu da ‘yan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng