Hajjin Bana: An Sanya Ranar da Alhazan Najeriya Za Su Fara Dawowa Gida

Hajjin Bana: An Sanya Ranar da Alhazan Najeriya Za Su Fara Dawowa Gida

  • Alhazan Najeriya da na sauran kasashen duniya sun kammala aikin hajjin shekarar 2026 a kasa mai tsarki watau Saudiyya
  • Hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON), ta bayyana shirinta kan fara jigilar mahajjata zuwa gida Najeriya
  • An sanar da cewa za a fara jigilar Alhazan Najeriya domin dawowa gida daga Saudiyya a ranar 5 ga watan Yunin 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Birnin Makka, Saudiyya - Hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da lokacin fara jigilar da mahajjata zuwa gida Najeriya.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa za a fara aikin jigilar dawo da mahajjatan Najeriya gida daga Masarautar Saudi Arabia ranar 5 ga watan Yuni, 2026.

Za a fara dawo da Alhazan Najeriya gida
Maniyyata daga Najeriya na kokari hawa jirgi Hoto: @hajjreporters
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce daraktan horarwa da bincike na hukumar, Farfesa Abubakar Abubakar, ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ban-girma ga Amirul Hajj na jihar Kano, Dokta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a garin Makka.

Kara karanta wannan

Hajjin 2026: Gwamnan Sokoto ya gwangwaje mahajjata da kyautar Sallah

NAHCON ta kammala shirye-shirye

Farfesa Abubakar ya ce an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da dawo da mahajjatan Najeriya cikin kwanciyar hankali, aminci, da kuma ba tare da samun kowane irin cikas ba bayan kammala ibadar aikin hajjin na shekarar 2026.

A cewarsa, NAHCON, ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomin kula da walwalar mahajjata na jihohi, kamfanonin jiragen sama, da kuma hukumomin ƙasar Saudiyya, sun tsaurara matakan da suka dace domin tabbatar da jigilar mahajjata cikin tsari don komawa Najeriya.

Za a dawo da Alhazan Najeriya gida

Ya bayyana cewa an tsara jadawalin dawowar ne cikin tsanaki domin rage jinkiri da cunkoso a filayen jiragen sama, tare da tabbatar da jin daɗi da lafiyar mahajjata a duk tsawon lokacin aikin.

Jami'in na NAHCON ya yaba da haɗin kan da aka samu daga jami'an jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da ke da hannu a aikin hajji, inda ya bayyana aikin na wannan shekara a matsayin ɗaya daga cikin mafi tsari a cikin lokutan baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Ana tsoron bullar cutar Ebola mai hadari a Kano, Borno da wasu jihohin Najeriya

Farfesa Abubakar ya kuma shawarci mahajjatan da su ci gaba da kasancewa masu ladabi da juriya, inda ya lura cewa nasarar aikin dawowar ya dogara ne ga babban mataki na haɗin gwiwa tsakanin mahajjata da jami'ai baki ɗaya.

An yaba wa hukumar NAHCON

Yayin da yake mayar da martani, Amirul Hajj na jihar Kano, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, ya nuna jin daɗinsa ga hukumar NAHCON saboda jajircewarta wajen kula da walwalar mahajjatan Najeriya a kasa mai tsarki.

Za a dawo da Alhazan Najeriya gida
Alhazai daga Najeriya na shirin hawa jirgin sama Hoto: @stanley_nkwocha
Source: Twitter

Ya yaba wa hukumar kan ci gaban da aka samu a lokacin ayyukan hajjin na shekarar 2026, musamman a ɓangarorin haɗin gwiwa, masauki, da kuma sufuri.

Amirul Hajj ya tabbatar da cewa mahajjata daga jihar Kano za su ci gaba da bin ƙa'idojin da aka kafa tare da ba da haɗin kai ga jami'ai domin tabbatar da samun nasarar tafiyar dawowa gida.

An ba Alhazan Sokoto kyauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya gwangwaje Alhazan jihar da kyautar kudi.

Gwamna Ahmed Aliyu, ya ba da gudunmawar Riyal 1,000 na ƙasar Saudiyya ga mahajjatan jihar da ke Saudiyya.

Ahmed Aliyu ya ba da kudin wadanda suka yi daidai da kusan naira 450,000, ga kowane daga cikin mahajjata 2,410 daga jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com