Mai Dokar Barci: Sojoji Sun Damke 'Dan Bijilanti da Zargin Yi wa ISWAP Leken Asiri
- Dakarun sojin Najeriya sun kama wani dan sa-kai da ake zargi da yi wa mayakan ISWAP leken asiri tare da taimakonsu a jihar Yobe
- Ana zargin mutumin na da hulɗa da ‘yan ta’adda tare da ba su bayanai a asirce wanda ke kassara kokarin jami'an tsaro wajen yakar ta'addanci
- Sojoji sun ce ana ci gaba da bincike kan wanda ake zargin a hedikwatarsu bayan an yi amfani da dabaru wajen cafke mutumin da ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe - Dakarun rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar mafarauta sun kama wani mutum da ake zargi da yi wa kungiyar Boko Haram/ISWAP leken asiri a karamar hukumar Damaturu ta jihar Yobe.
Majiyoyin soji sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai suna Alhaji Ibrahim, mai shekaru 42, da 3.05 na rana a ranar 25 ga watan Mayu, 2026.

Source: Twitter
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazaola Makama, wanda ya wallafa a shafinsa na X cewa bayan samun bayanan sirri kan alakar mutumin da ayyukansa tare da ‘yan ta’adda ne aka bi sawu, aka yi ram da shi.
Sojoji sun kama 'dan bijilanti a Yobe
Rahotanni sun nuna cewa mutumin yana cikin kungiyar ‘yan sa-kai da ke aiki a makarantar mata ta gwamnatin tarayya, GGUC da ke Damaturu a jihar Yobe.
Majiyoyin sun ce jami’an tsaro sun samu bayanai da suka nuna cewa mutumin na hulɗa da wasu da ake zargi ‘yan kungiyar ISWAP ne, lamarin da ya sa aka fara bibiyarsa kafin daga bisani a cafke shi.
An kuma bayyana cewa Alhaji Ibrahim ya fito ne daga kauyen Ahajiri da ke yankin Maisandari Ward a karamar hukumar Damaturu.

Source: Original
Bayan kama shi, an mika wanda ake zargin zuwa hannun jami’an sojoji domin a zurfafa bincike kan zargin da ake masa da kuma gano ko akwai wasu da suke da hannu a lamarin.
Majiyoyin sojin sun bayyana cewa wasu lokuta barazanar da al’umma ke fuskanta ba daga bakin mutane kawai take fitowa ba, har ma daga cikin mutanen da suke kusa da su.
Gargadin sojoji kan taimakon yan ta'adda
Rahoton ya ce jam'an tsaron sun ce akwai mutane da ke cin amanar al’ummarsu ta hanyar bai wa ‘yan ta’adda bayanai da kuma jefa rayukan bayin Allah cikin hadari.
Rahoton ya nuna cewa rundunar sojin Najeriya na ci gaba da kokarin ganin an dakile ayyukan leken asiri da taimaka wa kungiyoyin ta’adda musamman a yankunan Arewa maso Gabas da suka dade suna fama da matsalar Boko Haram da ISWAP.
A halin yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da karin bayani kan ko mutumin ya amsa zargin da ake masa ba, amma an tabbatar da cewa bincike yana gudana domin gano gaskiyar lamarin.
Sojoji sun yi yan ta'adda ruwan bama-bamai
A baya, mun kawo labarin cewa rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta ce hare-haren saman da ta kai sun kashe mayakan Boko Haram da dama tare da lalata muhimman sansanonin su.
Kakakin rundunar, Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026, yana mai cewa sun kai hari kan maboyar ‘yan tada kayar baya bayan an samu bayanai.
A cewar Ehimen Ejodame, an gudanar da hare-haren ne ranar Talata, 26 ga Mayu, bayan samun sahihan bayanan leken asiri da sa ido daga sama (ISR) tare da kammala shiri kafin a durar masu.
Asali: Legit.ng


