
Yan ta'adda







Gwamnatin Filato ta bayyana rashin jin dadin rahotannin da ke cewa dakarun DSS sun karbe wasu makamai da ta sayo domin yai da masu kashe mazauna jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar dan daba Baba Beru bayan an harbe shi da bindiga. An harbi Beru ne yayin da 'yan daba suka kai hari.

Gwamnan Binuwai ya bayyana cewa 'yan bindiga sun mamaye wasu yankuna a jihar, inda suke ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa suna salwantar da rayuka.

Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ta bulla a Arewa mai suna Mahmuda ta fara zafafa hare hare kan al'umma a Kwara. Sun fara kashe mutane a wurare daban daban.

Gwamna Alia ya ce maharan da ke kashe mutane a Benue ba 'yan Najeriya ba ne, suna amfani da AK-47, suna magana da bakon yare, kuma suna da mafaka a Kamaru.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang ya bayyana rashin jin dadin yadda ayyukan rashin tsaro ke ci gaba da kamari a sassa daban-daban da ke jihar tun daga 1999.

Gwamna Umaru Bago ya takaita zirga zigar abubuwan hawa da suka hada da babura da keke Napep a Minna. Ya ce za a rusa gidan da aka ba 'yan ta'adda mafaka a Neja

Gwamna Alia ya ce jihar Benue na fama da hare-haren 'yan ta’adda, inda ya roƙi al’umma su kai rahoton duk wani motsi ga jami’an tsaro don kare rayuka.

Yan bindiga sun tilasta wa ƙauyuka 12 da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara biyan harajin N60m bisa zargin ba sojoji bayanai da ke kawo musu tarnaki.
Yan ta'adda
Samu kari