Zamfara: An Hallaka Hatsabibin Ɗan Ta'adda da Aka Daɗe Ana Nema Ruwa a Jallo

Zamfara: An Hallaka Hatsabibin Ɗan Ta'adda da Aka Daɗe Ana Nema Ruwa a Jallo

  • Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta dakile harin ramuwar gayyan ‘yan bindiga a Mada, karamar hukumar Gusau da ke jihar Zamfara
  • Harin ya auku da safiyar ranar Laraba yayin da ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari domin daukar fansa kan samamen baya-bayan nan
  • Sojojin 'Operation Fansan Yamma' tare da jami’an sa-kai na Askarawa suka dauki mataki cikin gaggawa, suka shiga fafatawa mai tsanani da ‘yan ta’addan
  • Rundunar ta kashe ‘yan bindiga da dama ciki har da shugaban su Kachalla Dogo Idin Madu wanda ya shahara wajen kashe-kashe da satar mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jihar Zamfara ta yi wa ƴan bindiga ta'asa a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.

Rundunar ta dakile wani mummunan harin ramuwar gayya da ‘yan bindiga suka kai a Mada da ke Gusau a jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a hanyar Kaduna, an samu asarar rayuka

An yi ajalin rikakken dan bindiga a Zamfara
Rundunar sojoji ta yi nasarar hallaka ɗan bindiga a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

Sojoji sun yi raga-raga da yan bindiga

Majiyoyi na leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya auku da safiyar yau Laraba 12 ga watan Maris, 2025 lokacin da ‘yan bindiga suka mamaye Mada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan bindiga a wani artabu da suka yi a jihar Zamfara a cikin kwanakin nan.

Sojojin sun hallaka ƴan bindiga masu yawa bayan sun farmake su a sansaninsu da ke kasan wani tsauni a yankin Kaura Namoda.

Rahotanni sun ce jami'an tsaron sun yi raga-raga da ƴan bindigan bayan sun kai musu hari babu ƙaƙƙautawa ta sama da ƙasa.

Jami'an tsaro sun yi wa yan bindiga ta'asa a Zamfara
Dakarun sojoji sun hallaka wani rikakken dan bindiga a Zamfara. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Asali: Facebook

An yi nasarar hallaka hatsabibin dan bindiga

‘Yan ta’addan sun zo dauke da makamai, suna kokarin daukar fansa kan samamen da jami’an tsaro suka kai musu a baya-bayan nan.

Sai dai sojojin 'Opration Fansan Yamma' tare da 'yan sa-kai na Askarawa suka dauki matakin gaggawa, suka gwabza fada da ‘yan ta’addan nan take.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mayakan Lakurawa sun kashe mutane 13, sun kona ƙauyuka 7 a Arewa

Jami’an tsaro sun fi karfin ‘yan bindigar, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da kwato yankin daga hannun ta’addan.

Cikin wadanda aka kashe akwai Kachalla Dogo Idin Madu, wani shugaban ‘yan bindiga da aka dade ana nema ruwa a jallo.

An danganta Kachalla Dogo Idin Madu da kai hare-hare da dama, satar mutane da aikata munanan laifuka a fadin jihar Zamfara.

Samun nasarar kashe wannan babban shugaban ‘yan ta’adda zai taimaka wajen rage ayyukan ta’addanci a yankin da kewaye.

Sojoji sun yi wa ƴan bindiga barna a Zamfara

Mun ba ku labarin cewa dakarun sojoji da ke aikin samar da tsaro sun yi namijin kokari wajen samu nasara a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga a Zamfara.

Rahotanni sun ce sojojin sun hallaka wani shugaban dabar ƴan bindiga mai suna Yellow Aboki bayan sun yi arangama a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar.

Kara karanta wannan

Yaki da 'yan bindiga: Jami'an sojoji sun kashe 'Gwamna' a jihar Katsina

An ce tantirin ɗan bindigan dai ya yi ƙaurin suna wajen addabar mutanen da ke rayuwa a ƙauyukan da ke yankin Arewa maso Yamma na Tsafe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng