Bayan Alkawarin Gwamna kan Miyagu, Jami'an Tsaro Sun Hallaka Jagoran Lakurawa

Bayan Alkawarin Gwamna kan Miyagu, Jami'an Tsaro Sun Hallaka Jagoran Lakurawa

  • Jami’an tsaro tare da hadin guiwar ‘yan sa-kai sun kawar da jagoran ‘yan kungiyar Lakurawa, Maigemu a Kebbi bayan musayar wuta mai zafi
  • Majiyoyi sun ce an kashe Maigemu a Kuncin Baba a Karamar Hukumar Arewa, wani yanki mai wahalar shiga, a ranar Alhamis 6 ga watan Maris, 2025
  • Wannan nasara ta biyo bayan ziyarar Mai girma Gwamna Nasir Idris a Bagiza da Rausa Kade don jajanta wa iyalan wadanda ‘yan fashi suka kashe
  • A lokacin ziyarar, gwamnan ya yi alwashin inganta tsaro wanda yanzu aka kashe shugaban ‘yan fashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin-Kebbi, Kebbi - Jami’an tsaro tare da ‘yan sa-kai sun kawar da shahararren jagoran ‘yan bindiga na Lakurawa, Maigemu, a jihar Kebbi.

An tabbatar da kisan hatsabibin dan fashin daji, Maigemu a jiya Alhamis 6 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

Jami'an tsaro yi ajalin daya daga cikin jagoran Lakurawa
Jami'an tsaro sun hallaka wani shugaban Lakurawa a Kebbi. Hoto: Legit.
Asali: Original

An hallaka dan ta'adda, Shekau a Kaduna

Majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa an kashe Maigemu a yankin Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan fafatawa mai zafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan kisan wani daga cikin hatsabiban 'yan bindiga da yake kiran kansa da Shekau a kwanton-bauna a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce Shekau ya mutu ne yayin hari da wasu gungun 'yan bindiga na adawa suka shirya a Kachia da ke jihar.

Majiyoyi sun ce dan bindiga, Shumo ne ya kai farmakin domin daukar fansa kan Shekau, wanda ya kwace makamansa.

An tabbatar da cewa an kashe marigayi Shekau da wasu daga cikin yaransa a kwanton-bauna da aka kai masa ranar 5 ga Maris, 2025, a yankin kogin Narewo.

An yi nasarar hallaka wani jagoran Lakurawa a Kebbi
Jami'an tsaro a jihar Kebbi sun hallaka wani dan kungiyar Lakurawa da ake kira Maigemu. Hoto: HQ Nigerian Army, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu.
Asali: Facebook

An kashe dan Lakurawa bayan ziyarar Gwamna

Wannan nasara ta zo ne mako guda bayan Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya ziyarci Bagiza da Rausa Kade da yan ta'adda suka yi musu barna, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi

Gwamnan ya ziyarci yankunan ne don jajantawa al'ummar yankin kan kisan mutum shida da yan Lakurawa suka yi wanda ya tayar da hankulan mazauna garuruwan.

Mai girma Gwamnan yayin ziyarar, ya ba al'ummar yankin tabbacin samar da tsaro da kuma kare rayukansu daga yan bindiga da ma jama'ar jihar baki daya.

Wata majiya ta ce:

"A ziyarar gwamnan, ya ba da tabbacin daukar matakan tsaro, yau ga shi an kashe wannan jagora.
"Gawarsa tana nan a matsayin shaida ga sauran al'umma da yan ta'adda."

Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro a Kebbi

Mun ba ku labarin cewa ƴan bindiga sun yi ta'asa bayan sun kai wani harin ta'addanci kan ƴan sa-kai a jihar Kebbi.

An ce tsagerun ƴan bindiga sun yi wa ƴan sa-kan kwanton ɓauna ne bayan sun bi sawunsu domin ƙwato dabbobin da suka sace musu a yankin.

Rahotanni sun ce sojoji tare da haɗin guiwar ƴan sanda ne suka gano gawarwakin ƴan sa-kan a cikin daji da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng