Yaki da 'Yan Bindiga: Jami'an Sojoji Sun Kashe 'Gwamna' a Jihar Katsina
- Dakarun Operation Fansan Yanma sun yi raga-raga da wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Yusuf Gwamna, a Dutsin-Ma, Jihar Katsina
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an kuma halaka wasu ‘yan bindiga da dama a wannan farmaki da dakarun sojin Najeriya suka kai
- Dan bindiga Yusuf Gwamna ya dade yana addabar al’ummar Katsina da hare-hare da satar mutane kafin a kawar da shi a makon nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar kawar da wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Yusuf Gwamna, a wata fafatawa da suka yi a yankin Dutsin-Ma.
Rahotanni sun bayyana cewa, a yayin wannan samame da aka kaddamar, an kuma kashe wasu ‘yan bindiga da dama da ke aikata miyagun laifuffuka a yankin.

Asali: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Gwamna ya shahara wajen kai hare-hare, garkuwa da mutane da kuma aikata munanan laifuffuka a Katsina da wasu jihohi makwabta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakarun soji sun kashe Gwamna
Bisa bayanan sirri da aka tattara, dakarun soji sun kai farmaki kan sansanin ‘yan bindiga da ke Dutsin-Ma, suka yi raga-raga da Yusuf Gwamna tare da wasu na hannun damansa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan farmaki ya kasance wani gagarumin nasara a yaki da ‘yan ta’adda da ke addabar yankin Arewa maso Yamma.
Gwamna ya kasance daya daga cikin shugabannin ‘yan bindiga da suka fi haddasa tashin hankali a Katsina, kuma ya addabi jama’a da sace-sacen mutane da kona gidaje.
Nasarar sojoji na kara kwarin gwiwar jama’a
Kisan Yusuf Gwamna ya kawo sauki ga al’ummar yankin, domin tsawon shekaru yana rura wutar ta’addanci tare da tayar da hankulan jama’a.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu
Ana ganin cewa mazauna yankin za su nuna jin dadinsu bisa wannan gagarumar nasara tare da yaba wa jajircewar dakarun sojin Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya.
Jami'an tsaro za su ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ‘yan ta’adda har sai an murkushe su gaba daya a yankin Arewa ta Yamma.

Asali: Facebook
Kokarin kawar da ta'addanci a Arewa
A halin yanzu, rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin ci gaba da gudanar da hare-hare domin murkushe sauran ‘yan ta’adda da ke barazana ga zaman lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya na goyon bayan rundunar soji da kayan aiki don tabbatar da nasarar yakin da ake yi da ‘yan bindiga a fadin kasar nan.
A baya bayan nan dai jami'an tsaro sun cigaba da kai zafafan hare hare kan 'yan bindiga tare da kashe manya a cikinsu da kwato tarin makamai.
An kashe 'yan bindiga a Delta
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen gari sun yi gangami sun tunkari wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a cikin dajin da suka buya a jihar Delta.
A yayin farmakin da mutanen garin suka kai, sun samu nasarar kashe wasu 'yan bindiga uku tare da ceto wani mutum da suka sace kafin zuwan jami'an 'yan sanda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng