Sauki Ya Samu: Matatar Dangote Ta Yi Rangwame a Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

Sauki Ya Samu: Matatar Dangote Ta Yi Rangwame a Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

  • Matatar Dangote ta rage farashin kowace litar man fetur daga N1,275 zuwa N1,250 domin saukakawa yan Najeriya halin da ake ciki.
  • Matatar hamshakin attajirin da ya fi kowa kudi a Afiria, Aliko Dangote ta danganta matakin da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya
  • Duk da wannan rangwame, gidajen mai da dama har yanzu suna sayar da fetur sama da N1,350 a wasu yankunan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin kowace litar man fetur (PMS) daga N1,275 zuwa N1,250 a Najeriya.

Sabon farashin ya nuna raguwar kusan kashi biyu cikin ɗari, yayin da gasa ke ƙaruwa a kasuwar man fetur da gwamnatin tarayya ta tsame hannunta daga kayyade farashi.

Fetur.
Yadda ake zuba man fetur a cikin mota a wani gidan mai a Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Dalilin rage farashin fetur a Najeriya

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda cire tallafin mai ya hana Najeriya durkushewa

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa matatar ta yi wannan rangwame ne sakamakon ci gaba da faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Wani jami’in matatar ya tabbatar da matakin, yana mai cewa danyen mai shi ne babban kayan da ake amfani da shi wajen tace fetur.

Ya ce:

“Gaskiya ne mun rage farashin fetur a matatar Dangote saboda raguwar farashin danyen mai, wanda shi ne babban abin da muke amfani da shi wajen samar da man.”

Ya kara da cewa a kasuwar mai ta Najeriya da ke cin gashin kanta a yanzu, irin wadannan sauye-sauye abu ne da ya kamata a rika tsammani.

Dangote na iya kara rage farashin fetur

Jami’in ya bayyana cewa matatar na ci gaba da bibiyar halin da kasuwa ke ciki domin tabbatar da cewa farashin yana tafiya daidai da yadda abubuwa suke sauyawa.

A cewarsa:

“Har yanzu muna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a kasuwar danyen mai, kuma za mu ci gaba da yin gyaran farashi bisa ga yadda kasuwa ta nuna.”

Gidajen mai ba su sauya farashi ba

Kara karanta wannan

Babbar salla: Tinubu ya saukaka wa yan kasa, ya rage kudin sufurin jiragen kasa

Duk da rangwamen farashin da matatar Dangote ta sanar, bincike ya nuna cewa gidajen mai da dama a fadin kasar nan ba su fara aiwatar da sabon farashin ba.

A wasu yankuna, har yanzu ana sayar da litar fetur sama da N1,350, gwargwadon wurin da gidan mai yake da kuma kamfanin da ke sayar da man.

Masu amfani da man fetur na sa ran wannan ragun da aka samu zai sa farashin fetur ya sauka a gidajen mai nan gaba.

TUC ta nemi a karya farashin fetur

A wanu rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta TUC ta yi kira ga Gwamnatin Najeriya da ta dauki matakin saka tallafi a bangaren man fetur domin saukakawa talakawa.

TUC ta ce ce tun da gwamnatin tarayya ta dage cewa ba za ta dawo da tallafin fetur ba, dole ne shugabannin ƙasar su nemo hanyoyin rage raɗaɗin tashin farashin mai.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya fama da tsadar rayuwa, musamman bayan farashin man fetur ya tashi sosai a kwa nan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262