A Karshe, Hatsabiban Shugabannin 'Yan Bindiga Sun Ajiye Makamansu, Sun Mika Wuya
- Hatsabiban shugabannin 'yan bindiga, Abu Radde da Umar Black sun mika, sun saki fursunoni bayan matsin lamba daga sojoji
- An rahoto cewa sojojin Operation Fansan Yanma sun karya lagon ‘yan ta’adda, sun kulle hanyoyin tserewar miyagun a Arewa
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa Abu Radde da Umar Black sun hakura da ta’addanci ne bayan hare-haren sojoji da ya hana su sakat
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Wasu hatsabiban shugabannin 'yan ta’adda, Abu Radde da Umar Black sun ajiye makamanssu tare da mika wuya a Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa Abu Radde da Umar Black sun dade suna kai hare-hare da sace mutane a garuruwan Batsari da Safana.

Asali: Twitter
Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro da yaki da ‘yan tawaye a Tafkin Chadi, ya bayyana hakan a rahotonsa na kafar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin 'yan bindiga sun mika wuya
An ce shugabannin 'yan ta'addan sun kuma saki dukkanin mutanen da suka yi garkuwa da su yayin da suka mika wuya.
Hakazalika, sun mika wuya ne bayan hare-haren sojoji karkashin Operation Hadarin Daji da Operation Forest Sanity a yankin Arewa maso Yamma.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa sojoji sun tsananta hare-hare kan dabar Abu Radde da Umar Black wanda ya tilasta 'yan ta'addar mika wuya.
Rahoto ya ce 'yan ta'addar sun mika manyan makaman da suke aiki da su da suka hada da bindigogi tare da sakin mutane da suke tsare a sansaninsu.
Sojoji sun tsananta hare-hare kan 'yan bindiga
Wannan ci gaban ya biyo bayan karfafa ayyukan sojoji a Arewa maso Yamma, inda suke ci gaba da kai farmaki mai karfi kan sansanonin ‘yan ta’adda.
Hare-haren sama da na kasa sun jefa ‘yan ta’adda cikin rudani, wanda ya tilasta su tserewa cikin firgici daga sansaninsu tare da neman mafaka.
Rahotanni sun bayyana cewa manyan shugabannin 'yan ta’adda a Arewa sun tarwatse, kuma babu alamar za su iya sake hadewa saboda hare-haren sojoji.
Sojoji sun rufe hanyar tserewar 'yan ta'adda
An ce sojojin Najeriya sun kulle dukkanin wasu hanyoyin da 'yan ta'addar za su iya bi domin tserewa daga hare-haren.
Hakazalika, sojoji sun lalata hanyoyin samar da kayayyaki ga 'yan ta’addan, wanda ya kara raunana karfinsu na kai hare-hare a jihohin Arewa maso Gabas.
Wadannan nasarorin sun kara tabbatar da kudurin sojojin Najeriya na kawo karshen ta’addanci da mayar da zaman lafiya ga al’ummomin Arewa.
Bello Turji ya kafa sansani a Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa Bello Turji, fitaccen shugaban ‘yan bindiga, ya kafa sabon sansani a jihar Zamfara, bayan hare-haren sojoji.
Kafa sabon sansanin ya biyo bayan farmakin sojoji da ya jefa tawagar Turji cikin mummunan yanayi a Fakai da Shinkafi, inda suka tarwatse.
Rahotanni sun ce sansanin zai taimaka wajen kula da wadanda suka ji rauni da kuma tsare fursunonin da aka sace daga hare-hare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng