Gwamna Ya Kakaba N50m Ga Tinubu, Yan Takara Game da Kamfen 2027
- Gwamnatin Anambra ta sanar da sababbin tsare-tsare kan kuɗaɗen lasisin kamfen gabanin zaɓen 2027 a fadin jihar
- 'Yan takarar Sanata za su biya Naira miliyan 20, na Majalisar Wakilai Naira miliyan 5, yayin da na Majalisar Dokoki za su biya Naira miliyan 1.5
- Hukumar ta gargadi jam’iyyu da magoya baya kada su lalata kayan kamfen na abokan hamayya, tana mai jaddada hakan karya doka ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Gwamnatin Anambra ta hannun Hukumar Talla ta Jihar, ta bayyana sababbin tsare-tsare domin samun kudin shiga a jihar.
Hukumar ta bayyana kuɗaɗen lasisin kamfen na siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: UGC
Mataimakin Babban Manajan hukumar, Chika Ngobili, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Awka, cewar Punch.
Ngobili ya ce an shirya taron ne domin sanar da jam’iyyun siyasa da 'yan takara ka’idojin talla da kamfen a wuraren jama'a.
Kamfe: Miliyoyin da yan siyasa za su biya
A karkashin sabon tsarin, ɗan takarar shugaban ƙasa zai biya Naira miliyan 50, yayin da ɗan takarar Sanata zai biya Naira miliyan 20.
Haka kuma, ɗan takarar Majalisar Wakilai zai biya Naira miliyan 5, na Majalisar Dokoki Naira miliyan 1.5, shugaban ƙaramar hukuma Naira miliyan 2.5.
'Yan takarar kansila kuwa za su biya N100,000 kafin a ba su damar gudanar da kamfen a faɗin jihar.

Source: Facebook
Abubuwan da kudin lasisin suka shafa
Ngobili ya bayyana cewa kuɗin lasisin ya shafi fastoci, lasifika, motoci masu tambari, bainerori, takardun yaɗa bayanai, riguna da huluna.
Sauran abubuwan da tsarin ya ƙunsa sun haɗa da gangamin kamfen, rumfunan yaɗa manufofi, tarukan siyasa da sauran kayayyakin talla da aka amince.
Ngobili ya ce an fitar da ƙa’idojin ne bisa dokokin da ke tsara harkokin kamfen na siyasa da kuma shirin hukumar INEC na fara kamfen, cewar The Nation.
Ya ce hukumar tana sanar da jam’iyyu, 'yan takara, hukumomin talla, kafafen yaɗa labarai da jama'a sabbin ƙa’idojin talla na zaɓen 2027.
A cewarsa, hukumar ANSAA tana da ikon bayar da lasisi da izinin talla, kare kayayyakin gwamnati da kuma tara kuɗaɗen shiga.
Ya ƙara da cewa an ƙirƙiri tsarin ne domin tabbatar da tsari, rage gurɓatar gani, kare kadarorin jama'a da tabbatar da adalci.
Soludo ya hana malaman addini kudin al'umma
A baya, an ji cewa Gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya yi fatali da bukatar wasu malamin coci bayan sun nemi a kashe masu kudin al'umma.
Soludo ya ki amincewa da bukatar malaman na Katolika da suke ce gwamnati ta dauki nauyin yin riguna na musamman.
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudaden jama'a don riguna na kungiya ba, amma ya amince da tallafin ziyara zuwa gidajen marayu.
Asali: Legit.ng

