Dan Ta'adda Ya Yi Kokuwa da Soja domin Kwace Bindiga a cikin Daji

Dan Ta'adda Ya Yi Kokuwa da Soja domin Kwace Bindiga a cikin Daji

  • Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun kashe wani gagararran dan bindiga mai suna Hamisu Saleh a wani samame da suka kai jihar Filato
  • An taba kama Saleh a watan Disamba 2024 kan zargin kisan gilla da garkuwa da mutane, amma daga baya ya sake komawa aikata miyagun laifuffuka
  • Bayan an gudanar da bincike, Saleh ya amsa laifinsa tare da bayyana inda yake boye makamai, daga nan kuma ya tafi da sojoji domin nuna musu wajen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun samu nasarar kashe wani shahararren dan bindiga kuma mai garkuwa da mutane, Hamisu Saleh, wanda aka fi sani da “Master.”

Rahotanni sun nuna cewa an kashe shi ne a yayin wani samame da sojoji suka kai a yankin Barkin Ladi, jihar Filato.

Kara karanta wannan

NNPCL ya shirya hadaka da Rahama Sadau, Adam Zango da jiga jigan Kannywood

Dan bindiga
An harbe dan bindiga a jihar Filato. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi a kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa yadda aka kashe dan bindigar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi daga jami’an leken asiri sun tabbatar da cewa an gudanar da wannan samame ne a ranar 11 ga watan Fabrairu, 2025, domin dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.

A watan Disamba na shekarar 2024, an kama Saleh kan zargin kisan kai da garkuwa da mutane a Barkin Ladi.

Saleh ya amsa lafin garkuwa da mutane

Bayan da aka kama shi, Saleh ya amsa cewa shi ne ke da hannu a wasu hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Barkin Ladi.

Haka kuma, ya bayyana wasu wuraren da yake boye makamai da ake amfani da su wajen aikata laifuffuka.

Bisa bayanin da ya yi, dakarun OPSH sun shirya wani gagarumin samame a yankin Ropp na karamar hukumar Barkin Ladi da misalin karfe 8:47 na dare a ranar 11 ga Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

An shirya farmakin ne domin cafke sauran ‘yan kungiyar Saleh da kuma kwato makaman da suke amfani da su.

Saleh ya yi kokarin kwace bindiga

A yayin wannan aiki, Saleh ya yi kokarin yaudarar sojoji ta hanyar bayar da bayanan bogi kan inda ‘yan kungiyarsa da makaman suke.

Ana cikin tafiya da sojojin ne dan ta'addar ya yi yunkurin tserewa tare da kokarin kwace bindigar wani soja.

Sojojin da ke bakin aiki sun yi gaggawar daukar mataki, inda suka harbe Saleh har lahira kafin ya yi nasarar tserewa.

Sojoji za su cigaba da kai farmaki

Bayan kammala aikin, sojoji sun ci gaba da bincike a yankin domin gano karin makamai da kuma sauran ‘yan kungiyar Saleh, sai dai ba a samu karin makamai a wajen ba.

Dakarun OPSH sun tabbatar wa al’umma cewa za su ci gaba da gudanar da hare-hare da kuma bibiyar sauran ‘yan kungiyar domin dakile ta’addanci a jihar Filato baki daya.

Kara karanta wannan

Harsashi ya kare wa dan bindiga yana musayar wuta da sojojin Najeriya

Sojoji sun kama mai safarar makamai

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojan Najeriya ta cafke wata mota a cikin dajin jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa an kama motar ne tare da wani mutum daya da ake zargin mai safarar makamai ne ga 'yan ta'adda a Arewa ta Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng